Jump to content

Ummu Ayman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ummu Ayman
Rayuwa
Haihuwa unknown value
Mutuwa unknown value
Makwanci Al-Baqi'
Ƴan uwa
Abokiyar zama Ubayd ibn Zayd (en) Fassara
Zayd ibn Harithah
Yara
Sana'a
Aikin soja
Ya faɗaci Yaƙin Uhudu
Yaƙin Khaybar
yaƙin Hunayn
Imani
Addini Musulunci

Barakah bint Tha'alaba larabci بَـرَكَـة}, amfi saninta da Umm Ayman, ta kasance daya daga cikin wadanda suka karba musulunci da wuri. ta kasance yar asalin Habasha ce kuma baiwa ce ga iyayen Annabi Muhammad S.A.W, wato Abdullahi dan Abdul-Muttalib da kuma Amina yar Wahb. mijinta shine Ubayd dan Zayd na Banu Khazraj, wanda ta haifa mai Ayman dan Ubayd, sai ake kiranta da Umm Ayman

Bayan rasuwar Aminah, Baraka ta taimaka wajen renon Muhammad S.A.W. a gidan kakansa, Abd Al-Muttalib bn Hashim. Muhammad S.A.W ya kasance yana ganinta a matsayin uwa. Daga baya Muhammadu S.A.W ya 'yantar da ita daga bauta, amma ta ci gaba da yi ma sa hidima da iyalansa. Ta musulunta da wuri, kuma ta kasance a muhimman yakokin Uhudu da Khaibar.

Bayan samun 'yancinta, Muhammadu S.A.W ya shirya aurenta, na farko da Ubayd ibn Zayd na Banu Khazraj, auren da ta haifi ɗa, Ayman bn Ubayd, wanda ta dalilin shine aka yi mata alkunya da Umm Ayman (ma'ana mahaifiyar Ayman). Daga bayan Mutuwar Ubayd ibn Zayd, an aurar da ita ga dan riqon Muhammad S.A.W, Zayd bn Harithah. Inda ta haifi Danta tare da Zaidu, Usama bn Zaid, wanda ya yi aiki a matsayin kwamanda a sojojin Musulmi na farko, kuma ya jagoranci Yaki tare da Usama bin Zaid zuwa cikin Daular Rumawa.[1]

Baraka diya ce ga Tha’laba bin Amr, Bahabashe[1]. Ta yi hidima a gidan Abdullahi bn Abdil-Muddalib da Amina bint Wahb. Ta kula da Muhammad S.A.W, bayan rasuwar Amina[2].

Yarintar Muhammadu

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan rasuwar Aminah a Al-Abwa, Baraka ta kula da Muhammad S.A.W, kuma ta koma tare da shi zuwa gidan kakansa a Makka, inda ta yi masa hidima a lokacin yarinta [3] da kuma bayansa,[4] a lokacin girmansa[5]

Ibn Kathir ya ce, Abdullahi bn Abd al-Muttalib kakan Muhammad, ya ce wa Baraka kada ta yi sakaci da jikansa, musamman kamar yadda da yawa daga cikin Ahlul Kiṫâb (Larabci: أَهـل الـكِـتـاب, Ahlul Kitabi) suka yi hasashen zai kasance. Annabin al’umma[6].

Aure da yara

[gyara sashe | gyara masomin]

Lokacin da Muhammadu S.A.W ya auri Khadija, ya 'yanta Baraka, kuma ya bada auren ta, ga wani sahabi Khazraj mai suna Ubayd ibn Zaid. Ta hanyar wannan auren, Baraka ta haifi ɗa mai suna Ayman, don haka ake kiranta da "Umm Ayman" ("mahaifiyar Ayman").[7]. Daga baya kuma an kashe Ayman bn Ubayd a yakin Hunaini [8].

Dan renon Muhammad Zaid ibn Harithah daga baya ya auri Baraka. Suna da ɗa mai suna Usama wanda Muhammadu S.A.W ya naɗa a matsayin shugaban runduna kuma ya jagoranci nasarar yaƙi da Usama bin Zaid zuwa daular Rumawa[9].

Bayan Muhammadu S.A.W ya sanar da Annabcinsa, Ummu Ayman ta zama ɗaya daga cikin mabiyansa na farko. Daga baya sai ta yi hijira zuwa Madina. Ummu Ayman ta halarci yakin Uhudu. A inda ta debo wa sojoji ruwa tare da taimaka wa wadanda suka jikkata. Ta kuma raka Muhammad S.A.W a yakin Khaibar[10].

A yakin Uhud, mutane da yawa sun gudu zuwa Madina bayan jita-jitar mutuwar Muhammadu S.A.W. Ummu Ayman ta yayyafa wa wasu 'yan gudun hijira ƙura, ta ba su igiya, ta ce musu: "Ku ba ni takobinku da sandal ɗinku." Sannan ta nufi fagen fama tare da mata da dama[11]. Daga nan sai ta ji rauni da kibiya wadda Hebban binu Araqa, wani sojan makiya ya harba mata[12].

Dangantaka da sauran musulmin farko

[gyara sashe | gyara masomin]

Muhammad S.A.W ya kasance yana son Ummu Ayman, har yana tunaninta kamar uwa.[13] Hadisai da dama sun bayyana irin girmamawar da Muhammad S.A.W yake mata.[14] Ya ziyarci Ummu Ayman a gidanta, bayansa kuma halifofi Abubakar da Umar sun yi haka[15]. A wasu madogaran hadisi akwai sama game da falalar Ummu Ayman[16]. Haka nan an yabe ta a majiyoyin Shi’ah[17].

An ruwaito hadisi kadan daga gare ta[18]. Kamar su Anas bn Malik da Abu Yazid Madani da Hanash bn Abdullah San’any sun ruwaito daga gare ta[19].

Ba a bayyana ainihin ranar da Ummu Ayman ta rasu ba. Wasu sun ce ta mutu kimanin watanni biyar bayan rasuwar Muhammad S.A.W [20]. Amma a cewar ibn Sa’ad,[21] tana raye a farkon halifancin Uthman[22].

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


  1. 1.0 1.1 Zuhri, p 177; al-Tabarani, vol. 25, p. 86
  2. Ibn Sa`d, vol. 8, p. 223; Baladhuri, Vol. 1, p. 96
  3. Ibn Qutaybah, p. 150
  4. Baladhuri, vol.1, p.472
  5. Ibn Hajar, al-Ithaba, vol.8, p. 380
  6. ibn Kathir, al-Bidayah wa al-Nihayah, vol. 2, p. 343
  7. Ibn Sa`d, vol. 8, p. 223; Ibn Sa`d, vol. 4, p. 61
  8. mahallati, vol.2, p. 26
  9. Baladhuri, vol.1, p.96
  10. Al-Waqidi, Vol. 1, p. 241, 250, vol.2, p. 685; Ibn Sa`d, vol. 8, p. 225; Baladhuri, vol. 1, p.
  11. Bahr al-Ulum, MuhammadAli, translate by Muhammad Ali Amini,(1979), Woman of early Islam, Hekmat
  12. Ibn Athir, Ali (2009). al-Kamil fi al-Tarikh. vol. 2. Beirut: Dar Ihya al-Turath al-Arabi. p. 160.
  13. Ibn Sa`d, vol. 8, p. 223
  14. Ibn Sa`d, vol. 8, p. 223-226; Al-Dhahabi, vol. 2, p. 224
  15. Muslim ibn al-Hajjaj, vol. 2, p. 1907; Ibn Majah, vol. 2, p. 523-524; ibn Abd al-Birr, vol. 4, p. 1794
  16. Muslim ibn al-Hajjaj, vol. 2, p. 1907-1908
  17. Al-Kulayni, vol. 2, p. 405; Ibn Babawayh, p. 76
  18. Ahmad ibn Hanbal, vol. 2, p. 421; al-Tabarani, vol. 25, p. 87-91; Ibn Majah, vol. 2, p. 1107
  19. Ibn Hajar, vol. 12, p. 459
  20. al-Tabarani, vol. 25, p. 86; quoted from Zuhri.
  21. Ibn Sa`d, vol. 8, p. 226
  22. al-Tabarani, vol. 25, p. 86; Al-Dhahabi, vol.2, p. 227