Ummu Ammara (Nusaibah bint Ka'ab)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ummu Ammara (Nusaibah bint Ka'ab)
Rayuwa
Haihuwa Madinah
Makwanci Al-Baqi'
Ƴan uwa
Abokiyar zama Zaid bin 'Asim Mazni (en) Fassara
Yara
Sana'a
Imani
Addini Musulunci

Nusaybah bint Ka'ab ( Larabci: نسيبة بنت كعب‎  ; Hakanan ʾUmm ʿAmmarah, Ummu Umara, Ummu marah [1] ) tana ɗaya daga cikin matan farko da suka musulunta. Tana ɗaya daga cikin sahabban Annabi Muhammad (S A W) .

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Tana cikin ƙabilar Banu Najjar da ke zaune a Madina, Nusaybah 'yar'uwar Abdullah bin K'ab ce, kuma mahaifiyar Abdullah da Habib ibn Zayd al-Ansari.[1]

Lokacin da shugabanni, jarumai, da masu fada aji na Madina su 74 suka sauka a al-Aqabah don yin rantsuwar yin biyayya ga addinin Islama biyo bayan koyarwar sabon addinin da Mus`ab ibn `Umair ya yi a garin, Nusaybah da Umm Munee Asma bint ʿAmr bin ' Adi su kadai ne mata biyu da suka yi mubaya'a kai tsaye ga Annabi Muhammadu (S A W) . Mijin na karshen, Ghazyah bin ʿAmr, ya kuma sanar da Muhammad cewa matan ma suna so suyi mubaya'a da kansu, kuma ya yarda. [1] Ta koma Madina ta fara koyar da matan garin addinin Musulunci. Wannan mubaya'ah ko jinginar ita ce a zahiri ta ba da mulki ga Muhammad a kan birni, ta hanyar manyan jiga-jiganta. Matsayinta mafi shahara shi ne a yakin Uhudu, inda ta kare annabi. Ta kuma halarci yaƙin Hunain, Yamamah da Yarjejeniyar Hudaybia .

Rayuwar ta[gyara sashe | gyara masomin]

'Ya'yanta maza biyu, wadanda daga baya suka yi shahada a yakin, sun kasance ne daga aurenta na farko da Zaid bin ʿAsim Mazni. Daga baya ta auri bin ʿAmr, kuma ta haifi ɗa Tameem da ɗiya Khawlah. [1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 Ghadanfar, Mahmood Ahmad. "Great Women of Islam", Riyadh. 2001.pp. 207-215