Yaou Aïssatou

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yaou Aïssatou
Rayuwa
Haihuwa Tcheboa (en) Fassara, 28 Nuwamba, 1951 (72 shekaru)
ƙasa Kameru
Karatu
Makaranta University of Rouen (en) Fassara
Georgetown University (en) Fassara
Claremont Graduate University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Mai tattala arziki, ɗan siyasa, Mai kare ƴancin ɗan'adam da ɗan kasuwa
Imani
Jam'iyar siyasa Cameroon People's Democratic Movement (en) Fassara

Yaou Aïssatou (an haife ta a ranar 28 ga watan Nuwamba 1951) ita ce Darakta Janar na Kamfanin Zuba Jari na Ƙasar Kamaru (NIS). Ta kasance ministar harkokin mata ta farko a Kamaru.[1]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

Aïssatou ɗiyar lamido ce ta Tchéboa a yankin Arewa ta Kamaru, inda ta yi makarantar sakandare. Ta ci gaba zuwa Lycée Technique a Douala, inda ta sami digiri a cikin shekarar 1971. Bayan kammala karatunta ta yi karatu a fannin tattalin arziki a Jami'ar Rouen da ke Faransa, inda ta sami digiri na BA a shekarar 1975. Ta yi aiki tare da NIS a Kamaru na ɗan gajeren lokaci kafin ta tafi Amurka don yin karatu a Jami'ar Georgetown da Claremont Graduate School, ta kammala karatun MBA. [2]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Da ta koma Kamaru a shekarar 1979 ta koma NIS a matsayin mataimakiyar daraktar kuɗi. A watan Fabrairun 1984 aka ba ta muƙamin minista na farko a matsayin ministar harkokin mata ta Kamaru. Ta maye gurbin Delphine Zanga Tsogo a cikin watan Maris 1985 a matsayin shugabar ofishin ƙasa na kungiyar Mata ta Jam'iyyar Dimokuraɗiyyar Jama'ar Kamaru mai mulki, kuma an kara mata girma a watan Mayu 1988 zuwa matsayin ministar zamantakewa da harkokin mata, tana aiki har zuwa Afrilu 2000. [3] A shekara ta 2009 ne aka naɗa ta bisa umarnin shugaban ƙasa a matsayin sabuwar shugabar hukumar ta NIS, inda ta maye gurbin Esther Dang Belibi wacce ta yi murabus a cikin wata takaddama. [4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. DeLancey, Mark Dike; Mbuh, Rebecca; DeLancey, Mark W. (2010). Historical Dictionary of the Republic of Cameroon. Scarecrow Press. pp. 46–7. ISBN 978-0-8108-7399-5.
  2. Ngogang, Thierry. "Nomination: Yaou Aissatou rebondit à la Sni". Cameroon-Info.Net. Retrieved 16 November 2016.
  3. Foute, Rousseau-Joël. "SNI: les ambitions de Yaou Aïssatou". Cameroon-Info.Net. Retrieved 16 November 2016.
  4. "Esther Dang: La démission qui fait du bruit". Journal du Cameroun (in Faransanci). 2010-02-15. Retrieved 2021-01-28.