Jump to content

Yushau Shu'aib

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yushau Shu'aib
Rayuwa
Haihuwa 10 Oktoba 1969 (55 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Bayero
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a marubuci

Yushau Abdulhameed Shuaib,(an haife shi ranar 10 ga Oktoba, 1969) marubucin Najeriya ne. Marubuci ne,ma'aikacin hulɗa da jama'a kuma mai sharhi kan al'amuran jama'a kan al'amuran ƙasa da ƙasa, gami da batutuwa kamar aikin hulɗa da jama'a, daidaiton jinsi, tsaron ƙasa, ci gaban matasa, haƙuri da addini, fasahar watsa labarai da rigakafin laifuka. Ya wallafa labarai sama da 300 a cikin jaridun Daily Nigerian daban-daban a Najeriya.

Ya kammala karatunsa na Mass-Communicatia Jami'ar Bayero Kano, ya yi digirinsa na biyu a fannin Hulɗa da Jama'a a Jami'ar Westminster, London. Shuaib ya samu lambobin yabo da dama a fannin hulɗa da jama'a da fasahar rubutu.

Yushau Shuaib ya yi aiki a matsayin mai magana da yawun hukumomin gwamnati da suka haɗa da ma'aikatun yaɗa labarai, kudi da kuma kiwon lafiya na tarayya a lokuta daban-daban. Ya kuma taɓa zama shugaban yaɗa labarai da hulɗa da jama'a a hukumar tattara kuɗaɗen shiga da kasafi (RMAFC) da hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA).[1]

Bayan rubuta wata ƙasida mai cike da cece-kuce kan ministar kuɗin Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala kan yadda ake naɗa muƙamai a ma’aikatun gwamnati, gwamnati ta tilastawa Shuaib yin murabus.[2] A halin yanzu shi mawallafi ne kuma mai ba da shawara kan hulɗa da jama'a ga cibiyoyi masu mahimmanci a Najeriya.

Shuaib shi ne ya kafa kuma mai kamfanin Image Merchants Promotion Limited.[3][4]

  1. https://yashuaib.com/about-yashuaib/
  2. https://saharareporters.com/2013/03/05/still-okonjo-iweala-over-controversial-appointments-yushau-shuaib
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-08. Retrieved 2023-03-08.
  4. https://thenationonlineng.net/prnigeria-gets-global-pr-award/