Zaɓen Gwamnan Jihar Katsina, 2023

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentZaɓen Gwamnan Jihar Katsina, 2023
Iri gubernatorial election (en) Fassara
Kwanan watan 18 ga Maris, 2023
Ƙasa Najeriya
Applies to jurisdiction (en) Fassara Jihar Katsina

A shekarar 2023, alummar jihar Katsina zasu sake zaben sabon gwamna daga cikin 'yan takarar dake son zama gwamnan jihar a babban zaben 2023.[1]

Wadanda suka fito takarar daga jam'iyyu daban-daban sune:-

  1. Yakubu Lado: an haifi Yakubu a kauyen danmarke a karamar hukumar Funtua. yakubu lado gogagen dan siyasa ne ya fara takarar kansila kuma aka zabe shi, yayi takarar chiyaman na karamar hukumarsu kuma yaci zaben, sai yayi takararar danmajalissar tarayya kuma yaci zaben sai kuma yayi takarar sanata maikiltar Funtua zone kuma yaci. Sai dai yayi takarar gomnan katsina har sau 3 amma baici ba shine a 2023 ya kara dawo wa yake takara.[2]
  1. Dikko Radda= Ya kasance malamin makaranta tsakanin alif 1989-1999. Ya yi aiki a matsayin ma'aikacin banki tare da rusasshiyar bankin duniya na FSB tsakanin 1999-2003. Yayi Shugabancin Karamar Hukumar Charanchi ta Jihar Katsina tsakanin Jan 2005 zuwa Afrilu 2007. kuma an nada shi Shugaban Kwamitin riko na Karamar Hukumar Charanchi, a watan Mayun 2007. Sauran mukaman daya rike akwai; Babban Mai Taimakawa 'Yan Majalisu, NASS, Abuja, 2012-2014, Sakataren Jin Dadin Jama'a (APC), Yuni 2014-Yuli 2015. Ya rike sarautar gargajiya ta Gwagwar Katsina a masarautar KatsIna an nada shi a matsayin shugaban ma’aikata na Gwamnan Jihar Katsina. Shi ne Darakta Janar/Babban Babban Jami’in Hukumar Raya Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (SMEDAN). Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Dr Dikko Umaru-Radda karo na biyu a matsayin shugaban Hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana'o'i a Najeriya wato SMEDAN. Sanarwar ta fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a wata takarda mai dauke da kwanan watar 12 ga watan Maris na 2021. Dr. Dikko Umar Radda ya shiga siyasar neman kujerar Gwamnan Jihar Katsina, a siyasar 2023. A daidai lokacin ne ya ajiye shugaban Hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana'o'i a Najeriya wato SMEDEN [3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://dailytrust.com/katsina-govship-chances-weaknesses-of-apc-pdp-lp-nnpp-candidates/
  2. Yakubu lado - Wikipedia
  3. Dikko Umaru Radda - Wikipedia