Jump to content

Zinat-un-Nissa Begum

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zinat-un-Nissa Begum
Rayuwa
Haihuwa Aurangabad, 5 Oktoba 1643
Mutuwa Delhi, 7 Mayu 1721
Makwanci Red Fort (en) Fassara
Ƴan uwa
Mahaifi Aurangzeb
Mahaifiya Dilras Banu
Ahali Zeb-un-Nisa (en) Fassara, Badr-un-Nissa Begum (en) Fassara, Mehr-un-Nissa (en) Fassara, Zubdat-un-Nissa (en) Fassara, Sultan Muhammad Akbar (en) Fassara, Bahadur Shah I (en) Fassara, Azam Shah (en) Fassara, Kam Bakhsh (en) Fassara da Muhammad Sultan of Mughal (en) Fassara
Sana'a
Imani
Addini Musulunci
Mabiya Sunnah

Zinat-un-Nissa Begum ( Persian 5 Oktoba 1643 - 7 ga Mayu 1721) gimbiya Mughal ce kuma 'yar Sarki Aurangzeb ta biyu da babban abokinsa, Dilras Banu Begum . Mahaifinta ya ba ta lakabi mai daraja na Padshah Begum . :14,318

Zinat-un-Nissa Begum ("zinariya a cikin Mata") an haife ta a ranar 5 ga watan Oktoba shekara ta 1643, mai yiwuwa a Aurangabad, ga Dilras Banu Begum, matar farko ta Aurangzeb kuma babbar uwargidan. Mahaifiyarta gimbiya ce ta shahararriyar daular Safawad ta Farisa kuma diyace ga Mirza Badi-uz-Zaman Safavi, mataimakiyar Gujarat . Kakan mahaifinta shi ne sarki Mughal na biyar Shah Jahan wanda a zamaninsa aka haife ta. Zinat-un-Nissa tana da zurfin sanin rukunan Musulunci, kamar yadda yayarta, Gimbiya Zeb-un-Nisa da kanwarta, Gimbiya Zubdat-un-Nissa Begum . Malamai da malamai masu zaman kansu ne suka koyar da ita, kuma ta ƙi yin aure, ta zaɓi ta cigaba da zama marar aure dukan rayuwarta.

Zinat ta kasance mai bin kanin ƙannenta, Muhammad Kam Bakhsh, wanda ta sami gafarar mahaifinta a lokuta da yawa. Ko da yake cikakken ɗan'uwanta, Azam Shah, yana da tsananin ƙiyayya gare shi. Ita kadai ce abokiyar mahaifinta a zamanin mulkinsa, tare da kuyanginsa Udaipuri Mahal . Itace mai kula da gidan mahaifinta a cikin Deccan na kwata na karni har zuwa mutuwarsa a shekara ta 1707. Ta tsira dashi shekaru da yawa, tana jin daɗin girmama magabata a matsayin abin tunawa da rai na babban zamani. :282

Gudunmawa ga gine-gine

[gyara sashe | gyara masomin]
Zeenat-ul-Masajidwanda Zeenat-un-Nissa ta gina, wanda ke cikin Daryaganj, Delhi .

Ansan Zinat-un-Nissa ta gina ayari goma sha huɗu. A lokacin da take da shekaru talatin da bakwai, ta gudanar da aikin gina gidaje da dama na babbar hanyar da ta hada Awadh da Bengal. Wannan yunƙurin da tayi yasa ta sami yabon mahaifinta. Ta kuma sa aka gina Zeenat-ul-Masajid ("Adon Masallatai") da kuɗinta a cikin c.1700 kusa da bangon kogi na Red Fort a Delhi, inda aka binne ta. Al’adar ta ce ta nemi kudin sadakinta daga wajen mahaifinta, ta kashe shi duka wajen gina masallaci. [1]

Zinat-un-Nissa Begum ta mutu a Delhi a ranar sha takwas 18 ga watan Mayu shekara ta1721 tana da shekaru saba'in da bakwai a duniya 77.

 

  • Zeenat Mahal
  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Mukherjee2001