Jump to content

Abacha (abinci)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abacha
Kayan haɗi Manja, albasa, kayan miya, crayfish as food (en) Fassara, Oil Bean Soup (en) Fassara, garden egg sauce (en) Fassara, peppercorn (en) Fassara, gishiri da Ogiri
Tarihi
Asali Najeriya
abincin abacha
Nau'in abinvhin abacha

Abacha wani nau'in abinci ne da ya samo asali daga ƙabilar Igbo a kudu maso gabashin Najeriya.[1][2][3]

Abincin Abacha ya shahara a yankin Gabashin Najeriya. Ana yin abincin ne ta hanyar amfani da busasshen rogo, (a yanka ƙanana kamar taliya/ko yadda ake gani hoto na wannan makalar). Ana ci a matsayin abun ciye-ciye ko cikakken abinci. [1] Archived 2021-11-15 at the Wayback Machine Abacha kuma ana kiransa Salat ɗan Afirka-(African salad), abinci ne mai dadi na yammacin Afirka wanda abincin ƴan asalin ƙabilar Igbo ne (mutanen Igbo) kuma yawanci ana shirya shi da dabino, crayfish, ugba, da dai sauransu.

  • Busasshen rogo (yankakke mutsi-mutsi)
  • Ugba ko ukpaka
  • Man dabino
  • Powdered potash
  • Kifi (wanda aka dafa da kayan kamshi)
  • Ponmo (dafaffe kuma yankakken)
  • Albasa (yankakka)
  • Yalo (yankakke)
  • Ganyen kwai (yankakke)
  • Gishiri da busashen barkono
  • Crayfish
  • Mai dunkule-(Maggi)
  • Calabash nutmeg
  • Ogiri
  • Ganyen utazi
  • Tafasashshen Ruwan[1]

Yanda ake dafawa

[gyara sashe | gyara masomin]

1. A zuba rogo da aka daka (abacha) a cikin kwano na ruwa, a jika na tsawon mintuna 40 sannan a tsane ruwan.[4]

2. Bayan an yanka ganyen utazi, sai a soya kifi a tafasa ponmo. A zuba man dabino a cikin tukunya bayan an haɗa shi da potash a cikin ruwan dumi.[5][6]

3. Bayan sai a zuba kayan ƙamshi kamar yankakkun; albasa, barkono, iru, ugba da Yalo.[7]

4. Bayan ya dafu, sai azuba a wuraren cin abinci, aci abincin da ɗan zafi-zafin sa.

  1. 1.0 1.1 Ndeche, Chidirim (August 19, 2018). "HOW TO MAKE ABACHA (AFRICAN SALAD)". The Guardian. Archived from the original on November 15, 2021. Retrieved February 15, 2022.
  2. "Abacha: How to make your own African salad". Pulse Nigeria. October 31, 2021. Retrieved February 15, 2022.
  3. Collins, Nwokolo (September 28, 2021). "15 Amazing Health Benefits of Abacha (African Salad)". Health Guide. Retrieved February 15, 2022.
  4. Staff, Chef's Pencil. "African Salad/Abacha and Ugba Recipe". Chef's Pencil (in Turanci). Retrieved 2022-05-26.
  5. "Abacha(african salad) Recipe by Chinny's Kitchen". Cookpad (in Turanci). Retrieved 2022-05-26.
  6. "African Salad (Abacha and Ugba)". All Nigerian Recipes (in Turanci). Retrieved 2022-05-26.
  7. "How to Make Abacha (African Salad)". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2018-08-19. Archived from the original on 2021-11-15. Retrieved 2022-05-26.