Kudu ta Yamma (Najeriya)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kudu ta Yamma (Najeriya)
geopolitical zone of Nigeria (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Wuri
Map
 6°27′10″N 7°30′37″E / 6.4527°N 7.5103°E / 6.4527; 7.5103

Kudu ta Yamma (wanda aka fi sani da Kudu-maso-Yamma) ita ce daya daga cikin shiyyoyin siyasar Najeriya guda shida wanda ke wakiltar yankin siyasa na kudu maso yammacin kasar. Yankin ta ƙunshi jihohi shida – Ekiti, Legas, Ogun, Ondo, Osun, da Oyo.

Yankin tana kan tekun Atlantika daga kan iyakar kasa da kasa da Jamhuriyar Benin daga yamma zuwa Kudu ta Kudancin Najeriya daga gabas tare da Arewa ta Tsakiyar Najeriya daga arewa. Yankin Kudu maso Yamma ya rabu da tsakanin nau'in daji na "Central African mangroves" a gabar teku ta kudu yayin da manyan dazuzzukan cikin gida su ne Nigerian lowland forests da ke kudu da gabas tare da dajin Guinea-Savanna mosaic daga arewa maso yamma. Yanayin yankin ya bambanta tsakanin yanayi biyu na Najeriya; damina (Maris zuwa Nuwamba) da kuma lokacin rani (Nuwamba zuwa Fabrairu). Lokacin rani na zuwa da kurar (hazo) Harmattan; busasshiyar iska mai sanyi daga hamadar arewa tana kadawa cikin yankunan kudanci a wannan lokaci. A al'adance, yawancin shiyyar ta mamaye ƙasashen Yarbawa - ƙasar asali na kabilar Yarbawa, ƙungiyar da ke da mafi girman masu amfani da harshen a Kudu maso yammacin kasar.

Ta fuskar tattalin arziki, biranen Kudu maso Yamma – musamman biranen Legas da Ibadan – na bayar da gudunmawa sosai ga tattalin arzikin Najeriya yayin da aka bar yankunan karkara a baya. Yankin yana da yawan mutane kusan miliyan 47, kusan kashi 22% na yawan al'ummar ƙasar. Legas ita ce birni mafi yawan jama'a a Kudu maso Yamma kuma birni mafi yawan jama'a a Najeriya kuma birni na biyu mafi yawan jama'a a Afirka. Babban birni da kewayenta, ana kiranta da Lagos Metropolis Area, shine yanki na takwas mafi girma a duniya wanda ke da kimanin mutane miliyan 21; sauran manyan garuruwan kudu maso yamma sun hada da (bisa ga yawan jama'a) Ibadan, Ogbomosho, Ikorodu, Akure, Abeokuta, Oyo, Ifẹ, Ondo City, Ado Ekiti, Iseyin, Sagamu, Badagry, Ilesa, Obafemi Owode, Osogbo, Ikare da Owo .

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]