Abiodun Koya
| Rayuwa | |
|---|---|
| Cikakken suna | Abiodun Koya |
| Haihuwa | Ogun, 22 Disamba 1980 (44 shekaru) |
| ƙasa | Najeriya |
| Ƙabila | Yaren Yarbawa |
| Harshen uwa | Yarbanci |
| Karatu | |
| Makaranta |
University of the District of Columbia (en) The Catholic University of America (en) |
| Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
| Sana'a | |
| Sana'a |
opera singer (en) |
| Artistic movement |
gospel music (en) |
| Yanayin murya |
soprano (en) |
| Kayan kida | murya |
| Imani | |
| Addini | Kiristanci |

Abiodun (Abby) Koya (An haife ta aranar 22 ga Disamban shekara ta 1980) yar wasan gargajiya / opera, marubuciyar waƙa, mawaƙiya, 'yar wasan kwaikwayo, kuma taimakon jama'a ce wadda ke zaune a Amurka. Tana ɗaya daga cikin ƙwararrun mawaƙan wasan opera waɗanda suka fito daga Afirka. Abiodun Koya ya yi rawar gani a Fadar White House, a bikin rantsar da Shugaban kasa da kuma Babban Taron Demokradiyya. An haife ta ne a jihar Ogun ta Najeriya, mahaifinta ya karfafa gwiwa, wanda ya gabatar mata da kade-kade lokacin da take da shekaru uku, Koya ta zama mai sha'awar waka lokacin da ta cika shekara shida, tana kada goge da rera wakokin gargajiya a coci. Ta bar Nijeriya acikn shekara ta 2001 zuwa Amurka inda ta karanci Kasuwancin Kasuwanci a Jami’ar Gundumar Columbia, Washington, D.C Ta ci gaba da karatun wakoki don digirinta na biyu a Jami’ar Katolika, Washington. D.C.
Koya tana shugabantar wata kungiyar agaji kuma tana gudanar da ayyukanta na bada shawarwari.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]http://ladybrille.blogspot.lu/2008/05/africas-opera-divas-chinwe-enu-abiodun.html
http://www.vanguardngr.com/2013/05/abiodun-koya-set-for-the-big-stage/
http://news.wabe.org/post/nigerian-opera-singer-explores-classical-crossover-atlanta