Abiola Segun

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abiola Segun
Rayuwa
Haihuwa Lagos
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
Matakin karatu Digiri
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Yarbanci
Sana'a
Sana'a Jarumi, mai gabatar wa da marubin wasannin kwaykwayo
Muhimman ayyuka Tinsel (en) Fassara

Abiola Segun Williams ƴar fim ce ƴar Najeriya da aka fi sani da Titi K a rawar da ta taka a Talabijin na TV soap Tinsel.

Rayuwar Farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifeta a Lagos kuma anan ta girma. Abiola ta kammala karatunta na sakandare a shekarar 1983 sannan ta karanci fannin wasan kwaikwayo a jami’ar Obafemi Awolowo, Ile Ife. Ta fito a fina-finai da yawa kamar su "In the cupboard" daga Desmond Elliot, "I will take my chances" Emem Isong ya samar da Damages tare da Uche Jombo, Tana da aure kuma suna da yara biyu. Tana fama da cutar rashin kumburi wanda ke shafar fata da wasu gabobin jiki wanda ya fara wani lokaci a baya.[1]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Abiola Segun Williams ta zama ƙwararriyar ƴar fim daga 1986. Har ila yau, a makaranta ta fara wasan kwaikwayo don samun abin dogaro a matsayin kwararriyar 'yar wasan kwaikwayo. Mun yi abubuwa da yawa daga makaranta. A fagen sana'a, banda karatun zane-zane ba, na fara fita a matsayin dan wasan kwaikwayo a 1988, mun kawo wasannin kwaikwayo da yawa zuwa Lagos, Ibadan, Jos, Kaduna, da sauransu.

Fim ɗin ta na Farko shine wasan kwaikwayo - "Remilekun Jankarino" na Ben Tomiloju a 1986

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Olarewaju, Olamide. "Abiola Segun Williams: Tinsel actress opens up on dealing with Scleroderma" (in Turanci). Retrieved 2018-08-23.