Jump to content

Abu Ayyub al-Ansari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abu Ayyub al-Ansari
Rayuwa
HaihuwaMadinah, unknown value
ƙasaKhulafa'hur-Rashidun
Khalifancin Umayyawa
MutuwaConstantinople (en) Fassara, 674
MakwanciEyüp Sultan Mosque (en) Fassara
Sana'a
Sana'aSahabi
MambaAnsar (Musulunci)
Aikin soja
Ya faɗaciSiege of Constantinople (en) Fassara
Yaƙin Uhudu
Badar
Yaƙin gwalalo
Imani
AddiniMusulunci

Abu Ayyub al-Ansari[1] (Arabic:أبو أيوب الأنصاري, romanized: Abū Ayyūb al-Anṣārī, Turkish: Ebu Eyyûb el-Ensarî, ya rasu shekarar 674)[2] An haifi Khalid ibn Zayd ibn Kulayb ibn Tha'laba (Arabic:خالد ابن زيد ابن كُليب ابن ثعلبه, romanized: Khālid ibn Zayd ibn Kulayb ibn Thaʿlaba) a Yathriba/Madina, ya kasance daga ƙabilar Banu Najjar kuma ɗaya ne daga cikin manyan sahabban Annabi Muhammad S.A.W, Shi mutumin Madina ne kuma sune na farko a Madina da suka taimaka Annabi. Abu Ayyub yana daga cikin Ansar (Larabci: الانصار, ma'ana masu taimako, mataimaka ko masu tallafawa wani) a farkon tarihin Musulunci. Ansar su ne mutanen da suka goyi bayan Annabi Muhammad (SAW) bayan hijirarsa daga Makka zuwa Madina a shekara ta 622.

laƙabin Abu Ayyub yana nufin "uban Ayyub", domin kalmar Abu na nufin "uba" a larabci. Abu Ayyub ya rasu sakamakon rashin lafiya a lokacin yaƙin Farko na Larabawa da suka kewaye Konstantinoful(Constantinople).

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Abu Ayyub a Madina, a yankin Hijaz, da sunan Khalid bin Zayd. ya fito daga dangin Najjar, waɗanda suke daga cikin ƙabilar Banu Khazraj. Saboda Abu Ayyub shine shugaban iyalinsa, yana daga cikin dattawan Madina da aka zaɓa waɗanda suka je kwarin Aqaba, inda suka yi mubaya'a ga Musulunci a hannun Annabi Muhammad (SWA). Daga nan Annabi Muhammad ya sanya masa suna Abu Ayyub al-Ansari.

Bayan hijira, Annabi Muhammad (SAW) ya haɗa Muhajirun da Ansar a ƙarƙashin mubaya'a da haɗin kai guda.

Waqif na Masallacin Annabi

[gyara sashe | gyara masomin]

ƙasar da aka gina Masallacin Annabi (Al-Masjid an-Nabawi) a kanta, mallakin wasu marayu biyu ne, Sahal da Suhayl. Lokacin da suka sami labarin cewa Annabi Muhammad (SAW) yana son ya mallaki ƙasarsu domin gina masallaci, sai suka je wurinsa suka miƙa masa ƙasar a matsayin kyauta. Amma Annabi Muhammad (SAW) ya nace cewa zai biya kuɗin ƙasar, saboda su yara ne marayu. Daga ƙarshe, an amince da farashin sayen ƙasar, kuma Abu Ayyub al-Ansari ne ya biya kuɗin. Ta haka ne ya zama waqif(wato wanda ya kafa ko ya bayar da dukiyan a matsayin sadaka mai ɗorewa) na Masallacin Annabi a madadin Annabi Muhammad (SAW).

An kuma zaɓe shi a matsayin gwamnan Madina a zamanin Khalifa Ali ibn Abi Talib.[3]