Abubakar Gimba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

An haifeshi a garin lapai,Jahar Niger. Ya fara makarantar sa a Gulu Primary School daga shekarar 1959 zuwa 1962, sannan ya je Senior Primary School Lapai ya gama a shekarar 1964 kuma ya ci gaba inda ya sami takardar kammala kwaleji ta Government College Keffi daga 1965 zuwa 1969,Daga nan yayi jami'ar Ahmadu Bello Zaria daga shekarar 1970 Har zuwa shekarar 1974 inda yayi digirin shi na daya da na biyu,Sannan kuma ya halarce jami'ar Cincinnati wato University of Cincinmati a 1977 sai jami'ar lowa wato University of Iowa don program service. [4][5][6]

Aiki

Gimba yayi aiki a bankin Union sai kuma United Bank of Africa a masayin darakta me cikakken iko. (Prior to entering the corporate sector) Ya kasance ma'aikacin gwamnati wanda ya samu daukaka a tsakanin abokan aiki zuwa sakatare na dindindin a ma'aikata kudi a lokacin David Mark tsakanin 1984 zuwa 1987. Bayan ajiye aikin sa daga hidimar bankuna,an sa cikin masu aiki ko bada shawara wasu bangaren public institutions. An ba Gimba mukamin shugaban kwamitin ladabtarwa ta jami'ar Ahmadu Bello, lokacin makarantan yana tsakanin mulkin Mamman Kontagora.Daga nan sai, Abdulsalami Abubakar ya sa shi cikin wani kwamiti wato [Programme Implementation Monitoring Committee] har karshen lokacin shi a 1999. Gimba tsohon shugaban kungiyar Ahmadu Bello University alumni association sannan kuma daya daga cikin memba na Ahmadu Bello University Governing Council daga 2002 zuwa 2006. Shine farkon shugaban jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai. Ya zama me bada shawara ga shugaban majalisa David Mark akan tattalin arziki da abin da ya shafi kasafin kudi a 2010, sannan ya kasance me bada shawara akan abubuwa da dama,Ya taba aiki a kwamitin [presidential Review Committee on public service]. [7][8][9][1]