Abubakar Musa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Simpleicons Interface user-outline.svg Abubakar Musa
Governor of Kebbi State (en) Fassara

ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993
Patrick Aziza - Salihu Tunde Bello (en) Fassara
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Alhaji Abubakar Musa dan siyasan Najeriya ne wanda aka zaɓa a kan tsarin Jam’iyyar na kasa (NRC) a matsayin Gwamnan Jihar Kebbi, Najeriya, yana riƙe da muƙamin tsakanin Janairun shekarar 1992 da Nuwamban shekarata 1993 a lokacin Jamhuriya ta Uku ta Najeriya.[1][2][3][4]

Kafin ya shiga siyasa, Musa ya kasance Daraktan Kwastam. An zargi Musa da yin lalata da akwatunan zaɓe a zaɓukan Disambar 1991, amma lokacin da su ka yi shi hakika yana kasashen waje yana jinya. A watan Yulin 1993 ya kafa dokar kafa Kwalejin Ilimi ta Jihar Kebbi, yanzu ta zama kwalejin ilimi ta Adamu Augie.

A watan Yunin 2002 ya kasance ma'ajin ƙasa na sabuwar National Democratic Party (NDP). Ya kasance ɗan takarar da zai zama a jami'yar People Democratic Party (PDP) na gwamna a zaɓen 2003. A watan Janairun 2003 ya kasance a wurin wani taro inda Gwamnan Kebbi Muhammad Adamu Aliero ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a watan Afrilun 2003 a dandalin All Nigeria Peoples Party (ANPP).

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "ABOUT THE COLLEGE". Adamu Augie College of Education. Archived from the original on 2011-07-25. Retrieved 2010-04-30.
  2. "Now, to Real Politics". ThisDay. 2002-06-23. Archived from the original on 2003-10-21. Retrieved 2010-04-30.
  3. Kabir Dogon Daji (7 June 2002). "Kebbi: Aliero Battles Generals, Others". Weekly Trust. Retrieved 2010-04-30.
  4. Kingsley Nwezeh (2003-01-02). "Why I'm Seeking Re-election, By Aliero". ThisDay. Retrieved 2010-04-30.