Adamu Ciroma
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||
ga Yuni, 1999 - Mayu 2003 - Ngozi Okonjo-Iweala →
24 Satumba 1975 - 28 ga Yuni, 1977 ← Clement Nyong Isong - Ola Vincent (en) ![]() | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Potiskum, 20 Nuwamba, 1934 | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Harshen uwa | Hausa | ||||
Mutuwa | Abuja, 5 ga Yuli, 2018 | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Kwalejin Barewa | ||||
Harsuna |
Hausa Turanci Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a |
bureaucrat (en) ![]() | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |

Adamu Ciroma (an haife shi a ranar 20 ga watan Nuwanba, shekara ta 1934 kuma ya mutu a ranar 5 ga watan Yulin shekara ta 2018)[1] Ya kasan ce ɗan Nijeriya ɗan siyasa kuma Gwamnan Babban Bankin Nijeriya.An haife shi ne a birnin Pataskum dake Jihar Yobe[2].[3] Ya kasan ce memban Jam'iyyar People's Democratic Party ne har yayi wafati bai sauya sheka ba daga ((PDP)) .
Aikin jamhuriya ta biyu
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 1979, Ciroma yana daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa na jam'iyyar NPN ta kasa da suka tsaya takara a zaben fidda gwani na shugaban jam'iyyar, [4] wanda ake zaton gungun Mafiya Kaduna marasa fuska ne suka dauki nauyinsa, kungiyar da ake yada jita-jita ta 'yan boko daga Arewa, hafsoshi da jami'ai da ma’aikatan da aka jibge a kewayen Kaduna.[5] Ya zo na uku a zaben fidda gwani, bayan Shehu Shagari da Maitama Sule, wanda Hamza Rafindadi Zayyad shugaban kamfanin ci gaban New Nigeria ne ya dauki nauyin takararsa.[6]
Ciroma ya kasance sakataren NPN a takaice, sannan ya rike mukamin ministan masana'antu, noma da kudi a lokuta daban-daban. A matsayinsa na babban minista a gwamnatin Shagari, ya taka rawar gani wajen aiwatar da ajandar shugaban kasa musamman a fannin samar da abinci da kuma hada kai da hukumomin kasa da kasa wajen bunkasa shirin bunkasa noma (ADP).[7] A watan Satumba na 1983, an nada shi shugaban kwamitin mika mulki na shugaban kasa, wanda ya kara nuna amincewar da shugaban kasar ke da shi kan iyawar sa. An wajabta wa kwamitin ne ya gabatar da shawarwari kan yadda za a sake fasalin gwamnatin tarayya da ke cikin mawuyacin hali.[8]
Aikin Jamhuriya ta Hudu
[gyara sashe | gyara masomin]Ciroma dai ya kasance dan jam’iyyar PDP ne. Ya taba rike mukamin ministar kudi a gwamnatin Olusegun Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2003. A halin yanzu uwargidansa Maryam Ciroma ce ke rike da mukamin shugabar mata na jam'iyyar PDP ta kasa a Najeriya.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "BREAKING: Ex-Minister of Finance, Adamu Ciroma, died at 84". Archived from the original on 2018-07-05. Retrieved 2019-04-05.
- ↑ Bolaji Adepegba, Adamu Ciroma, tested and trusted yet uncrowned, Daily Independent Online, Nov 27, 2003 [1] Archived 2016-03-04 at the Wayback Machine
- ↑ Olajide Aluko. Nigeria and Britain after Gowon, African Affairs > Vol. 76, No. 304 (Jul., 1977), pp. 9
- ↑ Shehu Shagari. Beckoned To Serve. Heinemann Educational Books, Nigeria, 2001.pp214.
- ↑ Shehu Othman, Classes, Crises and Coup: The Demise of Shagari's Regime, African Affairs > Vol. 83, No. 333 Oct., 1984. pp 447, 449
- ↑ William Reno. Old Brigades, Money Bags, New Breeds, and the Ironies of Reform in Nigeria. Canadian Journal of African Studies > Vol. 27, No. 1 (1993), pp. 75
- ↑ Quentin Peel, "Shagari shuffles Cabinet", Financial Times, February 16, 1982.
- ↑ Quentin Peel, "President's party wins majority in Nigerian Assembly", Financial Times, September 6, 1983.