Adamu Talba Gwargwar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Adamu Talba Gwargwar
Senator Adamu Talba.jpg
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Rayuwa
Haihuwa Jihar Yobe, 15 ga Augusta, 1952 (69 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Adamu Garba Talba (an haife shi a ranar 15 ga watan Agustan shekarar 1952) tsohon sanata ne kuma dan siyasa a Najeriya da ya fito daga shiyyar arewa maso gabas. Dan asalin ƙabilar Karekaren da ake kira Birkayi ne kuma mahaifar sa ita ce garin Tikau dake karamar hukumar Nangere a Jihar Yobe. Yana ɗaya daga 'ya'yan marigayi tsohon Sarkin Tikau mai martaba Alhaji Abubakar Talba Shuwa sannan yana daya daga jerin masu sarautar gargajiya na fadar masarautar Tikau. Ya zama zaɓaɓɓen Sanata mai wakiltar shiyyar Yobe ta Kudu ne a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Karatu[gyara sashe | Gyara masomin]

Talba yayi karatun difloma a bangaren iya kula da gudanuwar mulki. Daganan sai ya shiga aikin gwamnati a jihar Yobe. Ya taba zama shugaban karamar hukumar Nangere sau biyu a jihar Yobe. An nada shi Shugaban Hukumar Gudanarwa, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Alare, kuma ya taba rike muƙamin Darakta na NNDC, Kaduna har wa yau kuma ya taɓa kasancewa Kwamishinan Lafiya na Jihar Yobe.

Ayyuka da Nasarori[gyara sashe | Gyara masomin]

A matsayinsa na Sanata, a watan Satumban 2008, Talba ya ba da shawarar kafa Kwamitin Hamada na Kasa don magance matsalar kwararar Hamada a yankin arewacin kasar.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]