Adewale Oluwatayo
Adewale Oluwatayo | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Adewale Oluwatayo (1950–2016) [1] ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazaɓar Ifako-Ijaye ta tarayya ta Legas. Ya yi shugaban ƙaramar hukumar Ifako-Ijaiye a tsakanin shekarun 2004 zuwa 2007. Ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara na musamman kan ilimi ga gwamnatin jihar Legas daga shekarun 2009 zuwa 2011. [2] [3] [4]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Adewale ya halarci makarantar nahawu ta Ilesha kuma a shekarar 1968, ya samu takardar shedar makarantar sa ta yammacin Afirka. Ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Najeriya da ke Nsukka a shekarar 1979. A shekarar 2005, ya sami takardar shaidar digiri na biyu a Jami'ar Jihar Legas. [1] [2]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Daga shekarun 2004 zuwa 2007, Adewale ya zama shugaban ƙaramar hukumar Ifako/Ijaiye. A tsakanin shekarar 2009 zuwa 2011, an naɗa shi a matsayin mai bawa gwamnatin jihar Legas shawara ta musamman kan harkokin ilimi a zamanin Gwamna Babatunde Fashola. [5] [6]
A shekarar 2015 ya lashe zaɓen majalisar wakilai ta tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar APC (All Progressive Congress) don wakiltar mazaɓar Ifako-Ijaiye na tarayya. [1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 vanguard (2016-07-21). "Lagos Rep, Adewale Oluwatayo is dead". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2024-12-10. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":1" defined multiple times with different content - ↑ 2.0 2.1 "House of Reps member dies". www.premiumtimesng.com. Retrieved 2024-12-10. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ BellaNaija.com (2016-07-21). "House of Reps Member Adewale Oluwatayo Passes On". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.
- ↑ Shibayan, Dyepkazah (2016-07-21). "House of reps member found dead". TheCable (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.
- ↑ Oluwagbemi, Ayodele (2016-07-21). "Lagos Rep, Adewale, dies". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.
- ↑ Sesan (2016-07-22). "Lagos Rep Elijah dies, Dogara, others mourn". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.