Jump to content

Afia Efere

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Afia Efere
miya
Kayan haɗi naman akuya, crayfish (en) Fassara, doya, seasoning (en) Fassara, gishiri, ruwa, Stockfish (en) Fassara da Peppered Ponmo (en) Fassara
Tarihi
Asali Najeriya
Afia Efere dage
Afia Efere da Abin hadi

Afia Efere miyar Najeriya ce da ta shahara a tsakanin kabilar Efik, miyar kuma ana kiranta da farar miya saboda ba a yinta da manja.[1][2]

Miyar Afia Efere

Farar miya ta samo asali ne daga kabilar Efik kuma tana kama da miyar Inyamurai 'Ofe Nsala' sai dai ana amfani da kayan miya kadan wajen yinta kuma ita Ofe Nsala ba a yinta da uyayak, maimakon haka Ofe Nsala' ana yinta ne da Utazi da Ogiri. Mutanen Calabar galibinsu kabilar Efik ne.[3]

Miyar wanda ba’a yinta da mai ana yinta ne da nama nau’i biyu naman akuya ko kaza kuma wannan shine dalilin da ysa ake kiranta da wasu sunayen kamar "Afiaefereebot" kuma "afiaefereunen" ma'ana farar miya da akuya da kuma farar miya da kaza.[4]

Sauran sinadaran da ake amfani da su wajen hada miyar sun hada da uyayak, Ehu (Calabash nutmeg), ganyen uziza, crayfish da da makamantansu

  • Nsala miyar
  • Ikot Udo Abia
  1. "How to Make Afia Efere In One Hour". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2018-04-15. Archived from the original on 2022-06-29. Retrieved 2022-06-29.
  2. "Afia Efere". ResearchGate.
  3. "I grew up eating fresh food - Ijeoma Onwudiwe". Vanguard News (in Turanci). 2011-06-17. Retrieved 2022-06-29.
  4. isaac (2013-12-12). "Dishes You Must Try Out In Calabar". Pulse Nigeria. Retrieved 2022-06-29.