Jump to content

Ahmad Aliyu Al-Huzaify

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ahmad Aliyu Al-Huzaify
Rayuwa
Sana'a
Sana'a qāriʾ (en) Fassara

Ahmad bin Ali Al-Hudhaify ɗaya ne daga cikin mahardata Alqur'ani mai girma kuma ɗaya daga cikin limamai da masu yin Khuɗuba a Masallacin Annabi Muhammad (S A W) da wasu Masallatan a ƙasar Saudiyya, ɗan liman kuma mai yin Khuɗuba a Masallacin ma'aiki (S A W). Ali bin Abdul-Rahman Al-Huzaify, yana aiki a matsayin limami kuma mai Khuɗuba a Masallacin Annabi da ke Madina bayan ya kasance limami kuma mai Khuɗuba a masallacin Quba na Madina, kuma malami ne a jami’ar Taibah da ke Madina, kuma ya yi aiki a Jami'ar Musulunci da ke Madina, inda ya samu digiri na biyu da digirin digirgir inda ya fita da sakamako mai kyau sosai, wanda ya fita ne da first class, ya halarta majalisin karatuka da dama da laccoci da taron ƙarawa juna sani a ciki da wajen Madina.[1]

A cikin watan Ramadan na shekara ta, 1438, Babban Shugaban kwamiti mai kula da harkokin Masallacin Harami da Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina ta sanya Al- Hudhaifi ya jagoranci masu Al'ummar Musulmi a cikin Sallar Tarawihi a Masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, inda yaci gaba da gudanar da Jagorantar Sallah Tarawihi/Asham/Alkayeji a cikin watan Ramadan a shekarar, 1439 AH da 1440 AH. A shekara ta, 1441 bayan hijira, a ranar 13 ga watan Safar aka yanke shawarar nada shi a matsayin limamin masallacin Annabi a hukumance.

A cikin watan Disambar shekarar, 2022, an ba da izini don ya gabatar da Khuɗuba a Masallacin Annabi.

  • Yayi karatu a wajen Malamai da dama, ƙarƙashin jagorancin Ahmad Al-Zayyat, inda ya samu shaidar iya karanta Al-qur'ani a cikin ruwayar Hafsu daga Imam Asim bin Abi Al-Nujoud.
  • Ya kuma yi karatu a wajen Baban shi wato Ali bin Abdulrahman Al-Hudhaifi.
  • Kuma ya ɗauki Ilimi mai ɗinbin yawa kama daga abinda ya shafi Kufa a Larabci, Hadisi, Tafsiri, Fikihu, da ƙa'idojin Fiqhu daga wajen Shehunan Malamai da dama a masallacin Annabi, Madina, da sauransu, baya ga karatun jami’a da yayi.
  1. "تكليف نجل الشيخ الحذيفي بإمامة المصلين في صلاة التراويح بالمسجد النبوي" (in Larabci). Akbaar 24. 26 May 2017. Archived from the original on 15 July 2023. Retrieved 15 July 2023.