Ali Bin Abdul Rahman Al-Huzaify

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ali Bin Abdul Rahman Al-Huzaify
Rayuwa
Haihuwa Saudi Arebiya, 6 ga Afirilu, 1947 (77 shekaru)
ƙasa Saudi Arebiya
Harshen uwa Larabci
Karatu
Makaranta Jami'ar Imam Muhammad ibn Saud Islamic
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a Liman
Imani
Addini Musulunci
Ali Bin Abdur Rahman Al Huthaify

Ali Bin Abdur Rahman Al Huthaify (an haife shi a ranar 22 ga watan Mayu shekarar 1947) (Larabci; علي بن عبد الرحمن الحذيفي) yana daga cikin Limaman Saudiyya wato Masjid Alharamain kuma mai Khuɗuba a Masallacin Manzon Allah, (S A W) da ke Madina (Khateeb Al-Masjid an-Nabawi) tun a shekarar 1402 A.H har zuwa yanzu, kuma tsohon limamin Masallacin Quba. Yanada salon karatun Alqur'ani ahankali da kuma zurfi.[1]

Aiki da Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1972 ya kammala karatunsa na digirin farko a fannin shari'a a Jami'ar Musulunci ta Imam Muhammad bin Saud. A shekarar 1975 ya sami digiri na biyu a fannin shari'a a Jami'ar Al-Azhar, sannan ya yi digirinsa ta 3 a jami'ar. Ya kasance limami kuma mai yin khuduba (Khateeb) a Masallacin Quba a shekarar 1978.[2] A shekarar 1979 ya zama limamin Masallacin Manzon Allah (S A W) da ke a Madina (Al-Masjid al-Nabawi). A shekarar 1981 a cikin watan Ramadan an nada shi don ya jagoranci Sallah Tarawihi a Masallacin Harami, bayan karewar watan Ramadan sai ya koma Babban Masallacin Madina inda ya ci gaba da jagorancin Sallah.[3]

Duba Kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Ali Al huthaify - علي الحذيفي - Holy Quran on Assabile". www.assabile.com. Retrieved October 27, 2019.
  2. "أئمة المسجد النبوي - في العهد السعودي ١٣٤٥-١٤٣٦ | عبد الله الغامدي". October 27, 2015. Retrieved October 27, 2019 – via Internet Archive.
  3. "Biography - Ali Al Hudhaify - Islamise". www.islamise.co.uk. Retrieved October 27, 2019.