Aisha Lawal

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aisha Lawal
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Yara
Ahali uku
Karatu
Makaranta Lead City University
Harsuna Yarbanci
Turanci
Sana'a
Sana'a mai tsara fim da Jarumi
Imani
Addini Musulunci
IMDb nm12805928

Aisha Lawal Oladunni Jarumar shirye-shiryen fina-finan Najeriya ce, marubuciya kuma mai shirya fina-finai. An bata lambar yabon Mafi Alkawari na Shekarar (Yoruba) a 2014 City People Entertainment Awards, Mari kyawon jarumar a wajen rol (Yoruba) mafi hazaƙar jaruma a lambar girmamawa ta2015 Best of Nollywood Awards, mafi darajar jaruma a ɓanagren taruka (Yoruba).[1][2][3][4]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

Aisha Lawal ƴar asalin garin Ibadan ce, Jihar Oyo t, Najeriya kuma ta halarci makarantar Adeen International School da Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Ogbomoso. Aisha Lawal tana da sha'awar yin wasan kwaikwayo tun tana ƙarama, inda ta rika yin wasan kwaikwayo daban-daban. Daga baya Lawal ta halarci Jami'ar Lead City, inda ta samu digiri a fannin shari'a da digiri na biyu a fannin harkokin gwamnati.

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Aisha Lawal ta halarci makarantar Femi Adebayo ta J15 a fannin wasan kwaikwayo daga 2008 zuwa 2010 kuma ta koyi yadda ake wasa. Fim ɗinta na farko shine Adunmadeke inda ta fito a matsayin karuwa. Ta yi suna saboda rawar da ta taka a film ɗinIrugbin. Tun lokacin da ta yi suna, ta ci gaba da fitowa a kusan fiye da Film 100. Ta shirya fina-finai har goma kamar Imu Nika da Opon Ife.

Kwanan nan ta fito a cikin fim ɗin Love Castle (2021) da Kunle Afolayan Netflix movie Aníkúlápó (2022) a matsayin Olori Sunkanmi.

Rayuwa ta ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Aisha Lawal a gidan su su uku ne kuma ita ce ta biyu. Tanada aure da ɗiya mace. Musulma ce.

Fina-finan ta[gyara sashe | gyara masomin]

  • King of Thieves (2022)
  • Aníkúlápó (2022 film) (2022)
  • Love Castle (2021)
  • Survival of Jelili (2019)
  • Blogger's Wife (2017)
  • Simbi Alamala
  • Eregun
  • Jalaruru
  • Aiyepegba
  • Apala
  • Iyawo Kan
  • Okirika
  • Dilemma
  • Shadow
  • Nkan Inu Igi
  • Irugbin
  • Adunmadeke

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Reporter (8 September 2018). "Nominees For 2018 City People Movie Awards [FULL LIST]". City People Magazine (in Turanci). Retrieved 2022-10-05.
  2. "AMVCA 2016: Full nomination list". Africa Magic – AMVCA 2016: Full nomination list (in Turanci). Retrieved 2022-10-05.[permanent dead link]
  3. BellaNaija.com (6 June 2014). "Rita Dominic, Davido, Tiwa Savage, Majid Michel – 2014 City People Entertainment Awards Nominees". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 2022-10-05.
  4. lawal, fuad (14 December 2015). "See full list of winners". Pulse Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-10-05.