Jump to content

Ajibade Omolade

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ajibade Omolade
Rayuwa
Haihuwa Najeriya, 12 ga Yuni, 1984 (40 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
El-Kanemi Warriors F.C.-
Enyimba International F.C.2002-2008
Gombe United F.C.2008-2008
Kungiyar Al-Hilal (Omdurman)2009-2009
Mighty Jets F.C. (en) Fassara2010-2010
Plateau United F.C. (en) Fassara2011-2011
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya

Ajibade Aji Omolade (an haife shi a watan Yuni 12, 1984)[1] ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Najeriya.

Omolade ya fara sana'ar sa ne da kungiyar El-Kanemi Warriors a Maiduguri jihar Borno. Ya koma Enyimba International FC A matsayin kyaftin ɗin ƙungiyar, Omolade ya jagoranci ƙungiyar zuwa gasar zakarun nahiyar Afrika sau biyu kuma ya lashe gasar cin kofin CAF a 2003 da 2004. Hakazalika ya lashe kofin CAF Super Cup sau biyu tare da ƙungiyar.

Ya fara ficewa daga Najeriya a watan Yulin 2007, ƙungiyar 1. FC Koln, ta ta tuhumeshi[2] a ƙasar Jamus daga bisani ya dawo Najeriya ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Enyimba International FC ya buga wasanni kaɗan a can sannan ƙungiyar ta bayar ds aronsa zuwa kungiyar kwallon kafa ta Gombe United a gasar Firimiyar Najeriya.

A shekara ta 2009 ya koma kulob din Al Hilal Omdurman na Sudan kan kwantiragin yarjejeniyar shekaru huɗu. Bayan shekara ɗaya ya dawo Najeriya inda ya kulla yarjejeniya ta shekara daya da Plateau United a gasar Premier ta Najeriya. Daga baya ya koma Enugu Rangers. A shekarar 2013 ya shiga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Niger Tornadoes

Ayyukan kasa da kasa

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2000 ya wakilci Najeriya U20 a gasar cin kofin Afrika na yan kasa da shekaru 20 (U20) a Habasha.

Ya lashe kofin gasar CAF Champions League, 2003 tare da ƙungiyar Enyimba International FC

Ya lashe kofin gasar CAF Champions League, 2004 tare da ƙungiyar Enyimba International FC

Sau huɗu Najeriya ta lashe kofin Premier da ƙungiyar Enyimba International FC

Lashe kofin gasar Nigerian Coca-Cola F.A Cup da ƙungiyar Enyimba International FC

Lashe gasar kofin gasar zakarun Dan Sudanese F.A Cup tare da ƙungiyar Al-Hilal Omdurman

  1. "Aji Omolade :: Ajibade Omolade ::".
  2. "Fanclub Koelsche Boecke 05". www.koelsche-boecke.de. Archived from the original on 2011-07-19.