Alex Morgan
Alexandra Patricia Morgan Carrasco (an haife ta a ranar 2 ga watan Yuli, shekarar 1989) Ba'Amurikiya ce kuma yar'wasan ƙwallon ƙafa. Morgan yar'wasan gaba ce wadda take buga wasa a kulub din Orlando Pride a National Women's Soccer League (NWSL) da kuma ƙungiyar kwallon kafa na mata United States national team. Tun 2018, takasance itace mai jarragamar yan'wasan kungiyar tare da Carli Lloyd da kuma Megan Rapinoe.[1]
Jimkaɗan bayan ta kammala karatu a Jami'ar California, Berkeley, inda ta buga wasa ma California Golden Bears, Morgan an zaɓe tane na daya a 2011 WPS Draft daga Western New York Flash. Anan ne, ta fara buga wasanta a matakin kwararru, kuma ta taimakawa ƙungiyar ta lashe gasar lig. Morgan, tana da shekaru 22 a lokacin, itace mafi karancin shekaru a ƙungiyar ta a gasar 2011 FIFA Women's World Cup inda kungiyar ta kaiga mataki na biyu da lashe kyautar azurfa. A kuma gasar 2012 London Olympics taci ƙwallon daya ƙungiyar ta tasamu nasara a minti na 123rd a wasan gabda na karshe tsakanin su da ƙungiyar Canada. Ta kammala 2012 da ƙwallaye 28 da taimakon cin ƙwallo 21, inda takasance tare da Mia Hamm amatsayin yar'Amurka kacal data ci kwallo 20 da kuma samun taimakon cin ƙwallo 20 acikin shekara daya, kuma hakan yasa tazama na shida yar'wasan Amurka data ci ƙwallaye 20 acikin shekara daya. An bayyana ta U.S. Soccer Female Athlete of the Year kuma itace ta biyu FIFA World Player of the Year.
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Alex
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Kassouf, Jeff (October 3, 2018). "USWNT notebook: Scheduling, captains and other updates from World Cup qualifying camp". The Equalizer. Retrieved October 4, 2018.