Jump to content

Alhaji Gero

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Alhaji Gero
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 10 Oktoba 1993 (31 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
El-Kanemi Warriors F.C.2009-2009
Lobi Stars F.C. (en) Fassara2010-2011
  Ƙungiyar kwallon kafa ta Maza ta Najeriya ta 'yan kasa da shekaru 202012-2013156
Enugu Rangers2012-2013
Kaduna United F.C.2012-2012140
Östers IF (en) Fassara2013-2014369
  Viborg FF (en) Fassara2015-2016231
Östersunds FK (en) Fassara2016-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Lamban wasa 17
Tsayi 185 cm

Salisu Abdullahi "Alhaji" Gero (an haife shi a ranar 10 ga watan Oktoban shekarar alif ɗari tara da casa'in da uku 1993) dan wasan kwallon kafa ne a kasar Najeriya wanda kuma ke taka leda a matsayin dan wasan gaba na gungiyar Helsingborgs IF ta Sweden .

Harkar Kwallon kafa

[gyara sashe | gyara masomin]

Shekarun farko

[gyara sashe | gyara masomin]
Gero yana wasan U21 na farko don Östers IF akan Kalmar FF
Alhaji Gero

Gero ya fara buga kwallo a filin Kano kafin ya sanya hannu kan kwantiragin kwararrun sa na farko da El-Kanemi Warriors yana da shekaru sha shida. A shekara ta gaba ya koma Lobi Stars. [1] A lokacin kasuwar musayar 'yan wasa a tsakiyar kakar wasanni a watan Afrilun shekarar 2012, Gero ya koma Enugu Rangers daga Kaduna United, kuma ya zura kwallo a wasansa na farko a karawar da suka yi da Akwa United [2]wanda ya taimaka wa kungiyarsa ta tashi kunnen doki 1-1 wanda ya ba su damar samun nasara a wasan shekarar 2012 Nigeria Premier League.[3]


A watan Agusta na shekarar 2013, Gero ya sanya hannu kan yarjejeniya da Östers IF, ƙungiyar da aka koma Superettan don kakar wasan shekarar 2014 (mafi girma na 2 a Sweden).[4]

A cikin watan Disamba na shekarar 2014, kulob na Danish na Viborg FF ya ba da sanarwar cewa sun sanya hannu kan Alhaji a kyauta.[5] Ya buga wasanni goma sha biyar 15 kuma ya zura kwallo 1 a kakar wasa ta farko.

Alhaji Gero

A ranar 16 ga Janairu 2016, Viborg FF da Gero sun amince su ƙare kwangilar bayan ɗan ƙaramin lokacin wasa.

Ahali da Dangi

[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai kanin Gero mai suna Ahmad shi ma kwararren dan wasan kwallon kafa ne.

Jerin Wasanni Da Kwallaye

[gyara sashe | gyara masomin]
As of 10 July 2019.[6]
Appearances and goals by club, season and competition
Club Season League National Cup Continental1 Other2 Total
Division Apps Goals Apps Goals Apps Goals Apps Goals Apps Goals
Östers 2013 Allsvenskan 10 1 1 0 11 1
2014 Superettan 26 8 4 0 2 0 32 8
Total 36 9 5 0 2 0 43 9
Viborg 2014–15 Danish 1st Division 15 1 0 0 15 1
2015–16 Danish Superliga 8 0 2 2 10 2
Total 23 1 2 2 25 3
Östersund 2016 Allsvenskan 22 3 4 2 26 5
2017 24 2 5 1 11 2 40 5
2018 9 1 2 1 1 0 12 2
2019 13 1 0 0 13 1
Total 68 7 11 4 12 2 91 13
Esteghlal 2018–19 Persian Gulf Pro League 7 0 2 1 1 0 10 1
Helsingborgs 2019 Allsvenskan 0 0 0 0 0 0
Career total 133 17 20 7 13 2 2 0 168 26
  1. "I will move from Enugu Rangers to Europe - Alhaji Gero". Weekly Trust. Archived from the original on 14 August 2013. Retrieved 19 November 2013.
  2. "Alhaji Gero excited with his first goal for Enugu Rangers". Goal.com. Retrieved 2012-09-24.
  3. "NPL Star of the Week: Alhaji Gero". MTNFootball. Archived from the original on 2016-02-06. Retrieved 24 September 2012.
  4. "Rangers' Alhaji Gero joins Swedish side Osters IF". Goal.com. 10 August 2013. Retrieved 6 February 2016.
  5. Audu, Sammy (2014-12-19). "Alhaji Gero vows to 'shake' Europe after Viborg switch". African Football. Retrieved 2023-10-12.
  6. "Nigeria - A. GERO - Profile with news, career statistics and history - Soccerway".