Jump to content

Aliyu Wakili Boya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aliyu Wakili Boya
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

13 ga Yuni, 2023 -
District: Furore/Song
Rayuwa
Haihuwa 8 ga Yuni, 1978 (46 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Aliyu Wakili Boya (an haife shi a shekara ta 1978) ɗan siyasan Najeriya ne kuma lauya wanda ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazaɓar Fufore/Song a jihar Adamawa. Ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Fufore da kuma shugaban kungiyar ƙananan hukumomin Najeriya (ALGON) a jihar Adamawa. [1] [2]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Boya a ranar 8 ga watan Yunin 1978 a garin Malabu cikin garin Fufore. Ya yi karatun sa a jami'ar Maiduguri inda ya samu digirin sa na farko a fannin shari'a. Bayan haka ya kamalla karatunsa na shari'a a Makarantar Lauyoyi ta Abuja inda ya zama Barista. [3]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Boya shi ne babban mai taimaka wa tsohon Sanatan Adamawa ta tsakiya, Bello Tukur, tsakanin 2011 zuwa 2015. Daga baya kuma aka zaɓe shi a matsayin shugaban gudanarwa na Fufore. A daidai wannan lokacin ne aka naɗa shi Shugaban Kungiyar Ƙananan Hukumomi a Najeriya (ALGON) na Jihar Adamawa. [3] [4]

A lokacin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2023, Boya ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Fufore/Song a matsayin ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC). Ya yi nasara ne da kuri’u 4,632 inda ya kayar da abokin hamayyarsa wanda shi ne mai riƙe da kujerar, Mustafa Muhammed Saidu, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP. [5]

Laƙabi na gargajiya

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 1 ga watan Afrilu, 2018, Boya ya samu naɗin Sarkin Matasa na Adamawa daga Lamido Barkindo. Wannan matsayi ya naɗa shi a matsayin jagoran matasan Adamawa. A yayin bikin naɗin sarautar, manyan mutane irin su Sanusi Lamido, tsohon Sarkin Kano, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya mai riƙe da sarautar Wazirin Adamawa, sun halarta a matsayin baki. [6]

  1. "Hon. Aliyu Boya Wakili, others to be Conferred prestigious International Peace Award". THE AUTHORITY NEWS (in Turanci). 2024-06-23. Retrieved 2024-12-23.
  2. Reporter, Our (2024-07-18). "'Technical education should be nurtured for a prosperous future' | The Nation". The Nation Newspaper (in Turanci). Retrieved 2024-12-23.
  3. 3.0 3.1 "Adamawa Central Senatorial:Wakili Boya:A Man with glowing political feats". TG NEWS (in Turanci). 2018-08-02. Retrieved 2023-06-18. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  4. Daily, Peoples (2018-03-12). "100 Adamawa students paid scholarships, say LG chair - Peoples Daily Newspaper" (in Turanci). Retrieved 2023-06-18.
  5. "Adamawa state House of Representatives election results and data 2023 - Stears Elections". www.stears.co. Retrieved 2023-06-18.
  6. Ada, Ada (2018-12-16). "Adamawa youths set to fight against drug abuse, appoints Boya as patron". DAILY TIMES Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-06-18.