Augustine Aniebo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Augustine Aniebo
Gwamnan jahar kogi

ga Augusta, 1998 - Mayu 1999
Bzigu Afakirya - Abubakar Audu
Gwamnan Jihar Borno

1997 - ga Augusta, 1998
Victor Ozodinobi (en) Fassara - Lawal Haruna
Rayuwa
Haihuwa Umunze (en) Fassara, 23 ga Maris, 1950 (74 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Harshen Ibo
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen Ibo
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Augustine Aniebo (An haife shi a ranar 23 ga watan Maris 1950). Janar ne mai ritaya dan Najeriya wanda ya yi aiki a matsayin kwamandan soji na jihar Borno, Najeriya, a lokacin mulkin Janar Sani Abacha da mai gudanar da mulkin jihar Kogi daga watan Agusta 1998 zuwa 29 ga Mayu 1999 a lokacin mulkin rikon kwarya na Janar. Abdulsalami Abubakar, yana mika wa zababben gwamnan farar hula Abubakar Audu a ranar 29 ga Mayu, 1999, a farkon Jamhuriya ta Hudu ta Nijeriya.[1]

Gwamnan Jihar Borno[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin watan Mayun 1997, jami'an tsaron Najeriya, masu aiki tare da shugabannin addinin Islama sun kai hari kan wata majami'ar Kiristoci a Maiduguri, jihar Borno inda suka kori limamin cocin da membobin cocin. Shugabannin cocin sun roki Aniebo da ya gaggauta daukar mataki don kaucewa rikicin addini.  A shekarar 1998, ya ce an karfafa rundunar da ke yaki da fasa kwauri a jihar Borno don rage fasa kwaurin man fetur zuwa kasashen makwabta.[2]

Gwamnan Jihar Kogi[gyara sashe | gyara masomin]

Aniebo wanda aka nada a matsayin gwamnan jihar Kogi a watan Agustan 1998, Aniebo ya bar ofis a ranar 29 ga Mayu 1999 ba tare da ya rantsar da wanda zai gaje shi ba, ya mika shi ta hannun wakili.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]