Lawal Haruna

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lawal Haruna
Gwamnan Jihar Borno

ga Augusta, 1998 - Mayu 1999
Augustine Aniebo, Mala Kachalla
Rayuwa
Haihuwa 1957 (66/67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Script error: The function "infoboxTemplate" does not exist.

Wing Kwamandan (mai ritaya) Lawal Ningi Haruna ya kasance gwamnan soja a jihar Borno, Najeriya daga watan Agusta 1998 zuwa May 1999 a lokacin mulkin rikon kwarya na Janar Abdulsalami Abubakar, ya mika wa zababben gwamnan farar hula Mala Kachalla a watan Mayun 1999. 

An nada Kyaftin Haruna a matsayin mai kula da Jihar Borno a watan Agustan shekarar 1998. Dole ne ya shawo kan takaddama kan tambayar koyar da Ilimi na Addinin Kirista a makarantun gwamnati, wanda shugabanin musulmai a jihar da galibin Musulmi suka yi adawa da shi. A ranar 3 ga Nuwamban 1998, ya ba da sanarwar cewa za a fara koyar da Musulmi da Kirista daban a makarantu tare da isassun ɗaliban Kirista, kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. A ranar 11 ga watan Disamba tarzomar ta biyo bayan kiran da wani Limami ya yi na kai wa Kiristoci hari, tare da asarar dukiya mai yawa amma babu mutuwa. A watan Yuni na shekarar 1999, an bukaci Haruna ya yi ritaya, kamar sauran tsoffin masu gudanar da mulki na soja.

A watan Disambar shekarar 2000, Haruna ya yi zargin cewa Lt-General Jeremiah Useni ya shirya kashe Shugaban kasa Janar Sani Abacha, wanda ya mutu a sanadiyyar dalilai a ranan 8 ga watan Yuni 1998.

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]