Jump to content

Ayo Omidiran

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ayo Omidiran
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

Rayuwa
Haihuwa 10 Nuwamba, 1963 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello Digiri a kimiyya : Biochemistry
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da legislator (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa All People's Congress (en) Fassara

Ayo Hulayat Omidiran, (An haife ta ranar 10 ga watan Nuwamban, 1965). 'yar siyasan Najeriya ce kuma 'yar majalisar tarayya mai wakiltar mazabar tarayya ta Ayedaade/Irewole/Isokan na jihar Osun. Ita memba ce ta jam'iyyar All Progressive Congress. Ta kasance ‘yar asalin Ikire ce a cikin karamar hukumar Irewole ta jihar Osun.[1]

Ta halarci makarantar Ayedaade Grammar School Ikire, a jihar Osun sannan ta samu takardar shedar kammala karatun ta na yankin Afirka ta Yamma (WAEC) a 1980. Daga nan ta wuce Jami’ar Ahmadu Bello zaria sannan ta kammala karatun digiri na farko a fannin Biochemistry a shekarar 1985.

Ta tsaya takarar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar tarayya ta Ayedaade / Irewole / Isokan a shekarar 2011 kuma tayi nasarar lashe zaben. Ta sake tsayawa takara a shekara ta 2015 kuma an sake zaben ta a karkashin inuwar jam’iyyar APC. Ta rike mukamai da dama a majalisa ciki har da Mataimakiyar Shugaban, Kwamitin Majalisar kan Wasanni; memba na Kwamitin Majalisar kan Shari'a, Sadarwa, Cikin Gida, Abubuwan Ma'adanai Masu Kauri, Harkokin Mata da Mata a Majalisar.[2]

Gudanar da Wasanni

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2002, ta zama memba a Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya kuma ta ci gaba da zama a can har zuwa 2005. Tun daga 2006, ta kasance mamba a kwamitin mata na FIFA . Ta zama mai mallakar Omidiran Babe, wata kungiyar kwallon kafa ta mata a Osogbo, jihar Osun a shekarar 1997. A 2017, an nada ta shugabar Hukumar Kwallon Kafa ta Mata ta NFF (NFF).[3]

Ta kasance mai sha'awar kwallon kafa. Ta dauki nauyin gasar Kwallan Kafa ta Mazabar Tarayya ta Ayedaade-Irewole-Isokan a farkon shekarar 2018 wacce ta kammala da wasan karshe a Ayedaade High School, Ikire, Jihar Osun.[4]

  1. "Hon (Mrs) Ayo Omidiran - The Official Website Of The State Of Osun". Archived from the originalon 2018-07-09. Retrieved 2018-07-03.
  2. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". Nass.gov.ng. Archived from the original on 2018-07-03. Retrieved 2018-07-03.
  3. "Akpodonor, Gowon (7 November 2017). "Omidiran's return will stabilize Nigerian women football, says Mabo". Retrieved 3 July 2018.
  4. Anonymous (29 March 2018). "Omidiran football fiesta thrills Osun community". The Guardian Nigeria (online). Retrieved 3 July 2018.