Bala James Ngilari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bala James Ngilari
gwamnan jihar Adamawa

1 Oktoba 2014 - 29 Mayu 2015
Umaru Fintiri - Bindo Jibrilla
Majalisar Wakilai (Najeriya)


District: Michika
Rayuwa
Cikakken suna Bala James Ngilari
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Bala James Ngilari lauya ne kuma ɗan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Adamawa, Najeriya daga ranar 1 ga watan Oktoban 2014 zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2015. Shi ne mataimakin gwamna daga shekarar 2012 zuwa 2015 a ƙarƙashin Murtala Nyako, Bindo Jibrilla ne ya gaje shi, wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa a 2015. Wata babbar kotun Yola ta yanke wa Ngilari hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zaɓin biyan tara ba bisa samunsa da laifin almundahana, amma ba da daɗewa ba kotun ɗaukaka ƙara ta wanke Ngilari kuma ta sake shi.[1][2][3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]