Umaru Fintiri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Umaru Fintiri
gwamnan jihar Adamawa

29 Mayu 2019 -
Bindo Jibrilla
gwamnan jihar Adamawa

15 ga Yuli, 2014 - 1 Oktoba 2014
Murtala Nyako - Bala James Ngilari
gwamna

Rayuwa
Cikakken suna Ahmadu Umaru Fintiri
Haihuwa Madagali, 27 Oktoba 1967 (56 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Mutanen Marghi
Harshen uwa Fillanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Harsuna Turanci
Fillanci
Hausa
Marghi
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Ahmadu Umaru Fintiri shine gwamnan Jihar Adamawa maici ayanzu.[1] Gabanin yakasance gwamnan Adamawa, dan'majalisa ne na Majalisar jihar, kuma ya riƙe muƙamin kakakin majalisar. Fintiri ya taɓa zama gwamna na wucin gadi na jihar Adamawa Najeriya, bayan tsige gwamnan lokacin Murtala Nyako a watan Yulin 2014,[2][3] inda daga baya Bala James Ngilari ya maye gurbinsa bayan watanni uku da yayi akan mulki.[4]

Fintiri ya lashe zaɓen gwamna na jihar Adamawa wanda aka gudanar a ranar 9th na watan Maris 2019, sai dai an bayyana zaɓen amatsayin wanda ba'a kammala ba, saboda yawan soke-soke da hukumar zaɓe tayi.[5] [[Umaru Fintiri ya tabbata zaɓabben gwamna da nasarar da yasamu a zagaye nabiyun zaɓen da aka gudanar da kuri'u 376,552.

inda ya kada abokin takararsa gwamna maici Jibrilla Bindow na jam'iyar All Progressives Congress (APC) wanda shi kuma ya samu ƙuri'u 336,386.[6].

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https:punchng.com/breaking-inec-declares-pdps-fintiri-winner-of-adamawa-governorship-election/amp/
  2. Tukur, Sani. "Adamawa Speaker, Umaru Fintiri, sworn in as Acting Governor". Premium Times. Retrieved 15 February 2019.
  3. Olaotan, Falade. "EXCLUSIVE: Why Adamawa PDP flag bearer, Umaru Fintiri's name appeared on Buhari's travel ban list". The News Guru. Retrieved 15 February 2019.
  4. Musa, Njadvara. "Fintiri, Buni win tickets in Adamawa, Yobe". Guardian. Retrieved 15 February 2019.
  5. Channels TV. Channels Television "Inec declares Adamawa governorship election inconclusive"
  6. https://www.channelstv.com/2019/03/29/breaking-pdps-fintiri-wins-adamawa-governorship-election/%7Cwebsite= Channels Television