Bamidele Olumilua

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bamidele Olumilua
Gwamnan jahar Ondo

ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993
Sunday Abiodun Olukoya (en) Fassara - Mike Torey
Rayuwa
Haihuwa 1940
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Mutuwa 4 ga Yuni, 2020
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Bamidele Isola Olumilua (1940 - 4 Yuni 2020) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya kasance zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ondo, Nijeriya daga Janairu 1992 zuwa Nuwamba 1993 a lokacin Jamhuriyyar Najeriya ta Uku,[1] da aka zaɓa a Jam'iyyarSocial Democratic Party (SDP). An tilasta masa barin muƙamin ne lokacin da mulkin soja na Janar Sani Abacha ya karɓi mulki. Ya yi aiki a matsayin jami'in diflomasiyyar Najeriya a wata jihar ƙasar Kanada.[2] Mataimakin gwamnan shi ne Olusegun Agagu, wanda daga baya ya zama gwamnan jihar Ondo daga 29 ga watan Mayu 2003 har zuwa Fabrairun Shekara ta 2009.[3] Ya kasance Chancellor, Jami'ar Jihar Ekiti.[4]

Olumilua ya koma jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a shekarar 1998. An naɗa shi Shugaban Hukumar Alhazai ta Kirista.[5] A watan Agusta 2005, PDP ta bayyana cewa shi ba ɗan jam’iyyar ba ne.[6] Daga baya ya zama ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar Action Congress (AC), wadda aka kafa a shekarar 2006.[7]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya mutu a ranar 4 ga watan Yuni, 2020, yana da shekara 80 a Duniya.[8]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Ex-Ondo governor, Bamidele Olumilua, is dead" (in Turanci). 2020-06-04. Retrieved 2022-03-19.
  2. "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2010-03-27.
  3. James Sowole (26 February 2009). "Ondo - Tale of a Titanic Electoral War". ThisDay. Retrieved 2010-03-27.
  4. "OLUMILUA BECOMES EKSU CHANCELLOR, PROF OSUNTOKUN PRO-CHANCELLOR". Archived from the original on 2012-03-14. Retrieved 2012-04-28.
  5. Ademola Adeyemo (10 November 2009). "Sixteen Years After - Where Are Babangida's Civilian Governors?". ThisDay. Retrieved 2003-03-27.
  6. Adesina Wahab (August 15, 2005). "Ekiti PDP disowns Olumilua". OnlineNigeria. Archived from the original on 2012-02-27. Retrieved 2003-03-27.
  7. "Atiku Must Apologise to AC - Olumilua". Daily Independent (Lagos). 23 March 2009. Retrieved 2003-03-27.
  8. "Ex-Ondo governor, Bamidele Olumilua, is dead" (in Turanci). 2020-06-04. Retrieved 2020-06-14.