Bandele Omoniyi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bandele Omoniyi
Rayuwa
Haihuwa 6 Nuwamba, 1884
ƙasa Najeriya
Mutuwa 1913
Yanayin mutuwa  (cuta)
Karatu
Makaranta University of Edinburgh (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a marubuci

Bandele Omoniyi (an haifeshi ranar 6 ga Nuwamba, 1884 – ya mutu a shekarar 1913) [1] ɗan Najeriya ne mai kishin kasa wanda aka fi sanin sa da littafinsa A Defence of the Ethiopian Movement a shekara ta 1908, ya buƙaci yi masa sauye-sauyen siyasa a ƙasashen da suka yi wa mulkin mallaka, yana mai gargadin cewa in ba haka ba juyin juya hali na ƙasar Afirka na iya kawo karshen mulkin Birtaniya.[2] A cewar Hakim Adi, yana ɗaya daga cikin misalan farko na dalibin Afirka ta Yamma mai fafutukar siyasa a Biritaniya.[3]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Bandele Omoniyi a birnin Legas, a Najeriya a yau, kuma iyayensa sun sayar da filayensu don biyan kuɗin karatunsa a Burtaniya, inda Omoniyi ya fara zuwa a shekaraa ta 1905. Ya shiga Jami’ar Edinburgh a shekarar 1906, don karantar ilimin shari’a, daga karshe ya daina karatunsa yayin da ya ƙara tsunduma cikin harkokin siyasa gadan-gadan, inda ya rungumi aikin jarida mai adawa da mulkin mallaka a cikin littattafan gurguzu, Scotland da Najeriya. [4] Ya rubuta wa 'yan siyasar Birtaniya daban-daban, ciki har da Firayim Minista, Henry Campbell-Bannerman, da kuma shugaban jam'iyyar Labour Ramsay MacDonald nan gaba, yana neman wakilci ga 'yan Afirka a yankunan da suka yi wa mulkin mallaka.

Sukar mulkin mallaka[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin a shekarar 1907 Omoniyi ya soki mulkin mallaka a cikin jerin wasiku zuwa ga Mujallar Edinburgh. Ya kuma rubuta labarai ga jaridun Afirka ta Yamma, kuma a 1908 ya buga babban aikinsa, A Defence of the Ethiopian Movement, a Edinburgh, yana sadaukar da shi "ga 'Yan Majalisar Dokokin Biritaniya Mai Girma da Girmamawa".[5]

An kama shi[gyara sashe | gyara masomin]

Daga baya Omoniyi ya koma Brazil a wajajen shekara ta 1910, inda daga bisani aka kama shi kan harkokin siyasa. Ya ƙi yarda da taimako daga Ofishin Jakadancin Burtaniya.[6] An ɗaura shi, ya kamu da cutar beriberi kuma ya mutu yana da shekaru 28.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Kevin Shillington, Encyclopedia of African History, Volume 1, Fitzroy Dearborn, 2005, p. 596.
  2. David Killingray, Africans in Britain, Frank Cass & Company, 1994, p. 109.
  3. Hakim Adi, "Bandele Omoniyi--A Neglected Nigerian Nationalist", African Affairs, Vol. 90, No. 361 (October 1991), pp. 581–605.
  4. Jeffrey Green, Black Edwardians: Black People in Britain 1901-1914, Frank Cass Publishers, 1998, p. 147.
  5. 5.0 5.1 Hakim Adi, "Omoniyi, Bandele", in David Dabydeen. John Gilmore, Cecily Jones (eds), The Oxford Companion to Black British History, Oxford University Press, 2007, p. 350.
  6. Adi, Kakim (December 1991). "Bandele Omoniyi – Student Politician". Association for the Study of African, Caribbean and Asian Culture and History in Britain Newsletter (2): 13–14.