Benard E. Aigbokhan
Benard E. Aigbokhan | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ewu (en) , 3 Oktoba 1952 (72 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
University of the West of Scotland (en) University of Paisley (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Malami da Mai tattala arziki |
Benard E. Aigbokhan malami ne ɗan ƙasar Najeriya, (an haife shi a ranar uku 3 ga watan Oktoba, shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin da daya 1951) kuma masani ne kan harkokin tattalin arziki.[1] Ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban jami'ar Samuel Adegboyega, Nigeria daga ranar bakwai 7 ga watan Janairu, shekarar alif dubu biyu da goma Sha ukku 2013 zuwa ranar shida 6 ga watan Janairu, shekarar alif dubu biyu da ashirin 2020.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Eronmonsele a Ewu Ishan, Edo, Nigeria ɗa ne ga dangin David Ikhifa da Comfort Otiti Aigbokhan a ranar ukku 3 ga watan Oktoba, shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin da biyu 1952. A cikin shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da takwas 1978 ya sami digirinsa a fannin tattalin arziki a Jami'ar Gabashin London, Ingila, da Master of science a fannin tattalin arziki a Jami'ar Stirling, Scotland, shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da tara 1979. PhD a fannin tattalin arziki ya zo a Jami'ar Yammacin Scotland, tsohuwar Jami'ar Paisley, Scotland, Aa shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyar 1985.[2]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Eronmonsele ya fara aikinsa ne a matsayin babban jami'i a ma'aikatar yaɗa labarai ta tarayya, jihar Legas daga shekarun alif dubu daya da dari tara da saba'in da biyu 1972 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da ukku 1973. Daga nan, ya tafi Scotland kuma ya yi aiki a matsayin mataimakin mai koyarwa a Jami'ar Paisley daga shekarun alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyar 1982 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyar 1985. Bayan haka, ya dawo Najeriya ne a matsayin malami a Jami’ar Jihar Imo a shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da shida 1986 sannan ya wuce Jami’ar Jihar Edo, Ekpoma, daga shekarun alif dubu daya da dari tara da tamanin da bakwai 1987 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da biyu 1992 a matsayin mai karatu. Ya zama farfesa a fannin tattalin arziki a shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da biyar 1995. Daga baya ya zama ma’aikacin Resource na kwamitin UNESCO na ƙasa a jihar Legas daga shekarun alif dubu daya da dari tara da tamanin da tara 1989 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da daya 1991 da cibiyar kula da harkokin tattalin arziki da gudanar da mulki a Ibadan, Najeriya, tun daga shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da daya 1991.[3]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Eronmonsele ya yi rubutu akan Tsare-tsare, Aiki da Rarraba Kuɗi a Najeriya a cikin shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da takwas 1988. Ya yi rubutu akan Ka'idar Macroeconomic, Policy and Evidence a cikin shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da biyar 1995. Ya yi aiki a matsayin Edita na Iroro Journal of Arts and Social Sciences daga shekarun alif dubu daya da dari tara tamanin da bakwai 1987 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da biyu 1992. Ya kasance Mai Ba da Gudunmawa a Global visions: Beyond New World Order a shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da uku 1993. Ya rubuta ayyuka goma Sha ukku 13 a cikin littattafai guda ashirin da ukku 23 a cikin yare guda daya tilo 1. Ya kuma halarci tare da gabatar da kasidu a yawancin tarurrukan ilimi.[4]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Eronmonsele ya auri Fummilayo Ogedengb a ranar ukku 3 ga watan Agusta, shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyar 1985. Sun rabu a watan Nuwamba shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da takwas 1988. Ya auri Rita Ekhuelohan Atoe a ranar biyu 2 ga watan Janairu, shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da daya 1991 kuma yana da 'ya'ya har guda ukku 3.[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "ANEEJ mourns Board Chairman, Prof Aigbokhan". Vanguard News (in Turanci). 2020-07-14. Retrieved 2022-03-04.
- ↑ "SAU ORGANISES INTERNATIONAL CONFERENCE IN HONOUR OF PROFESSOR BENARD AIGBOKHAN – SAU News" (in Turanci). Archived from the original on 2022-11-28. Retrieved 2022-11-28.
- ↑ "Bernard Eronmonsele Aigbokhan Archives". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Archived from the original on 2022-11-28. Retrieved 2022-11-28.
- ↑ "UNN Staff Profile". www.unn.edu.ng. Retrieved 2022-11-28.
- ↑ "UNN Staff Profile". www.unn.edu.ng. Retrieved 2022-11-28.