Biodun Oyebanji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Biodun Oyebanji
gwamnan jihar Ekiti

16 Oktoba 2022 -
Kayode Fayemi
Rayuwa
Haihuwa 21 Disamba 1967 (56 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Jami'ar jihar Ekiti
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Abiodun Ayobami Oyebanji,(an haife shi a ranar 21 ga watan Disamban shekarar 1967)ɗan siyasan Najeriya ne, ya kasance tsohon sakataren gwamnatin jihar Ekiti, shugaban ma'aikatan jihar kuma a halin yanzu shine zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ekiti.[1][2][3]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Oyebanji ya halarci Makarantar Sakandare ta Awo Community kafin ya koma C.A.C Grammar School da ke Efon-Alaaye, Jihar Ekiti, sannan ya koma Makarantar Fasaha da Kimiyya ta Tarayya a Jihar Ondo da Makarantar Sakandare ta koyon Kasuwanci da ke Aramoko, Jihar Ekiti (shekarar 1979 zuwa shekarar 1983).

A shekarar 1989, Oyebanji ya sami digiri na farko a Kimiyyar Siyasa (BSc.) Wato a turance ana cewa political science daga Jami'ar Jihar Ondo (Jami'ar Jihar Ekiti a yanzu, Ado-Ekiti ), sannan ya wuce Jami'ar Ibadan, Jihar Oyo a shekarar 1992 inda ya yi digirinsa na biyu. Degree (M.Sc) duka dai a Kimiyyar Siyasa.

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fara aiki a matsayin malami a Sashen Kimiyyar Siyasa, a Jami'ar Ado Ekiti a shekarar (1993-1997).

Bayan ya ɗan yi aiki a fannin ilimi, sai ya sauya sheka zuwa kamfanoni masu zaman kansu a matsayin Manaja, Ma'aji da kuma al'amuran da ya shafi harkokin kuɗi a bankin Omega Bank Plc (yanzu Bankin Heritage ) har zuwa Mayun shekarar 1999.

Aikin Gwamnati[gyara sashe | gyara masomin]

Biodun Oyebanji ya yi aiki a wurare daban-daban a aikin gwamnati ta hanyar naɗawa ko kuma a matsayin memba na kwamitoci.

A shekarar 1994 ne aka naɗa Oyebanji a matsayin sakataren kwamitin da aka kafa domin kafa jihar Ekiti, karkashin jagorancin Baba Deji Falegan.[4] Ya kuma kasance sakataren asusun raya jihar Ekiti a na wani lokaci.

Lokacin da Najeriya ta koma kan turbar dimokuradiyya a shekarar 1999, yana da shekaru 32, an naɗa shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan mashawartan Otunba Niyi Adebayo, wanda shi ne zaɓaɓɓen gwamnan jihar na farko a dimokuraɗiyya a jihar Ekiti. Oyebanji ya hau matsayi ne har ya zama shugaban ma’aikatan gwamnan jihar a shekarar 2003.

A shekarar 2009, an naɗa shi a matsayin shugaban hukumar gudanarwa, cibiyar horar da ƴan ƙasa da jagoranci a ƙarƙashin ma’aikatar matasa da ci gaban wasanni ta tarayya (Yuni shekarar 2009 – Disamba 2010).

A shekarar 2010, an naɗa Oyebanji a matsayin kwamishinan hade-hade da harkoki tsakanin gwamnati sannan daga bisani an naɗa shi a matsayin shugaban ofis na jihar na dabarun kawo canji a Ekiti (OTSD) shekara guda bayan gwamnatin Kayode Fayemi.[5]

A shekarar 2018, Kayode Fayemi ya naɗa Oyebanji sakataren gwamnatin jihar (SSG), bayan an zaɓe shi a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Ekiti.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2021, Oyebanji ya yi murabus daga mukaminsa na sakataren gwamnatin jihar domin cim ma burinsa na tsayawa takarar gwamna.

An yi ta raɗe-raɗin cewa Oyebanji ne wanda Kayode Fayemi ya fi so, wanda hakan ya sa aka samu raɗe-raɗin wani mataki da aka ɗauka a jihar wanda ya sa wasu masu neman tsayawa takarar gwamna suka janye daga zaɓen fidda gwanin takarar gwamna da suka yi zargin cewa "Kwamitin zaɓen ya kunshi magoya bayan Fayemi ne".[6][7]


Koke-koken sauran ƴan takarar da shugabannin jam’iyyar ba su samu karɓuwa ba, don haka ne aka gudanar da zaɓen fidda gwani, kuma Oyebanji ya samu kuri’u 101,703, ba tare da hamayya da shi ba a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ekiti da aka shirya gudanarwa ranar 18 ga watan Yunin shekarar 2022.

Rayuwarsa[gyara sashe | gyara masomin]

Biodun Oyebanji yana aure da Prof. (Mrs) Oyebanji , wacce mataimakiyar farfesa ce a jami'ar Ibadan kuma gimbiya a Ado Ekiti.[8][9]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Lawal, Sodiq (2022-06-19). "BREAKING: INEC Declares APC's Oyebanji Winner Of Ekiti Governorship Election (See Results)". The Nation Reporters (in Turanci). Archived from the original on 2023-06-09. Retrieved 2022-06-19.
  2. Lawan, Nuruddeen (18 June 2022). "Abiodun Oyebanji: Important Facts about Ekiti APC Governorship Candidate Who Wants to Succeed Fayemi". legit.ng.com. Retrieved 21 June 2022.
  3. "BREAKING: INEC declares Oyebanji winner of Ekiti governorship election". Punch Newspapers (in Turanci). 2022-06-19. Retrieved 2022-06-19.
  4. "Biodun Oyebanji: garlands for true Ekiti homeboy at 54 - The Nation Newspaper" (in Turanci). 2021-12-21. Retrieved 2022-06-19.
  5. "15 things to know about Ekiti Governor-elect Oyebanji". The Nation Newspaper (in Turanci). 2022-06-19. Retrieved 2022-06-21.
  6. "PROFILE: Biodun Oyebanji, the long-serving public officer who'll be next Ekiti governor". TheCable (in Turanci). 2022-06-20. Retrieved 2022-06-21.
  7. "Seven governorship aspirants withdraw from APC primary election in Ekiti". TheCable (in Turanci). 2022-01-27. Retrieved 2022-06-21.
  8. "15 things to know about Ekiti Governor-elect Oyebanji". The Nation Newspaper (in Turanci). 2022-06-19. Retrieved 2022-06-21.
  9. Ayeni, Tolulope (2022-06-19). "Biodun Oyebanji (BAO) biography: Ekiti Governor Elect Profile". KikioTolu News (in Turanci). Archived from the original on 2022-07-03. Retrieved 2022-06-19.