Jump to content

Caleb Femi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Caleb Femi
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 1990 (33/34 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of London (en) Fassara
Sana'a
Sana'a mai daukar hoto da marubuci
IMDb nm9178255

Caleb Femi (an haifeshi a shekara ta 1990) marubuci ne kuma ɗan Najeriya, ɗan ƙasar Burtaniya, mai shirya fina-finai, daukar hoto, haka-zalika tsohon ɗan takarar matasa na Landan. Kundin wakokinsa na farko, mai suna; Poor, an ba shi lambar yabo ta Forward Prize for Poetry.

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Femi a shekara ta 1990 a Kano, Nijeriya,[1] inda ya girma a wurin kakarsa.[2] Lokacin da yake ɗan shekara bakwai, ya yi ƙaura domin shiga cikin iyayensa a Arewacin Peckham Estate a Landan.[3] Bayan ya bar makaranta, ya karanci Turanci a Jami'ar, Queen Mary, University of London. [2]

Daga 2014 zuwa 2016 Femi ya koyar da Turanci a makarantar sakandare a Tottenham.[2] A cikin 2016 an zaɓe shi a matsayin wanda ya lashe kyautar matasa na farko a London.[4] A ranar 30 ga Yuli 2020, ya wallafa kundin waƙoƙinsa na farko, mai suna Poor,[5] wanda ya ci Kyautar Forward Prize's Felix Dennis Prize for Best First Collection a cikin watan Oktoban shekarar 2021.[6]

Kawo yanzu Femi ya yi kuma ya fitar da gajerun fina-finai guda huɗu, yana aiki a matsayin marubuci / darakta akan kowanne:[7]

  • And They Knew Light (2017)
  • Wishbone (2018)
  • Secret Life of Gs (2019)
  • Survivor's Guilt (2020)

An saka sunan Femi a cikin mujallar Dazed 2021 Dazed100, jerin tsarin sabbin masu tsara al'adun matasa.[8]

  1. McConnell, Justine (21 July 2017). "Caleb Femi". writers make worlds (in Turanci). Retrieved 16 November 2020.
  2. 2.0 2.1 2.2 Peirson-Hagger, Ellen (28 October 2020). "Caleb Femi: 'Poetry is the art of the people'". New Statesman. Retrieved 14 December 2020.
  3. Armitstead, Claire (30 October 2020). "Caleb Femi: 'Henceforth I'm solely preoccupied with being a merchant of joy'". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077. Retrieved 16 November 2020.
  4. Flood, Alison (3 October 2016). "Poet Caleb Femi named first young people's laureate for London". The Guardian. Retrieved 14 December 2020.
  5. "Poor by Caleb Femi". The Poetry Book Society (in Turanci). Retrieved 16 November 2020.
  6. Bayley, Sian (25 October 2021). "Kennard, Femi and Sealey win Forward Prizes for Poetry". The Bookseller. Retrieved 25 October 2021.
  7. "Caleb Femi". IMDb. Retrieved 20 October 2021.
  8. Dazed (6 April 2017). "Vote for Caleb Femi on the #Dazed100". Dazed (in Turanci). Retrieved 20 October 2021.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]