Catherine Obianuju Acholonu
Catherine Obianuju Acholonu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Orlu (Nijeriya), 26 Oktoba 1951 |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen, Ibo |
Mutuwa | Jahar Imo, 18 ga Maris, 2014 |
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (kidney failure (en) ) |
Karatu | |
Makaranta | University of Düsseldorf (en) |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci, researcher (en) , university teacher (en) , maiwaƙe da ɗan siyasa |
Catherine Obianuju Acholonu (an haifeta a ranar 26 ga watan Oktoba a shekara ta 1951 - ta mutu a ranar 18 ga watan Maris a shekara ta 2014) marubuciya ce 'yar Nijeriya, mai bincike kuma mai rajin siyasa.[1]
Ta yi aiki a matsayin Babban Mashawarciya ta Musamman (SSA) ga Shugaba Olusegun Obasanjo kan Fasaha da Al'adu, kuma ta kasance mamba ce ta kungiyar Marubutan Najeriya "Association of Nigerian Authors" (ANA).[2][3]
Kuruciya, Ilimi da aure
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Catherine daga dangin kiristoci Catholica Inyamurai, mahaifanta sune Chief Lazarus Emejuru Olumba da kuma Josephine Olumba da ke rayuwa a kauyen Umuokwara, birnin Orlu.[4][5] Itace babba diya acikin 'ya'ya hudu.[6]
Ta kammala karatun ta na firamare da sakandare a makarantan "Holy Rosary School", kana daga bisani kuma akai mata aure da Brendan Douglas Acholonu wanda ya kasance likita ne dake aiki a kasar Germany a wancan lokacin.[4][5]
Catherine daga bisani ta fara karantu a jami'ar University of Düsseldorf a matsayin dalibar Turanci, daga bisani ta karanta American literature da kuma Germanic linguistics a shekara ta (1974) inda tayi digiri dinta na biyu a shekara ta alif(1977). A cikin shekara ta alif(1982) ta kammala digirinta na uka a fannin yaren Igbo (Igbo Studies), a yayinda ta zama mace ta farko 'yar Afurka da ta fara kammala karatun Masters' da PhD a jami'ar Dusseldorf dake Germany. Ta halarci taronta na farko a Ibadan a shekara ta gaba akan "Pan Africanism", inda ta gabatar da takaddu hudu akan darasin.[6]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Malantaka
[gyara sashe | gyara masomin]Catherine ta koyar da turanci a kwalejin Alvan Ikoku Federal College of Education, dake birnin Owerri tun daga shekara ta (1978) sannan ta wallafa littattafai fiye da goma sha shida.[2]
Ta kirkiri AFA A journal of Creative Writing a shekara ta(1982) wanda shine mujalla na farko dangane da adabin harsunan Afurka. A shekara ta (1986) itace kadai 'yar Najeriya kuma su biyu 'yan Afurka da suka samu halartar shirin "United Nations Expert Group Meeting on 'Women, Population and Sustainable Development: the Road to Rio, Cairo and Beijing'.[4] Gwamnatin Amurka ta zabe ta a matsayin Fulbright Scholar a shekara ta (1990) a bisa aikin da tayi wajen tattara bayanai akan tushen Inyamurai dangane da Olaudah Equiano, wani shahararren mai haramtawa kuma masukin cinikayyar bayi) wanda ya zamo abun darasi ga sauran kwalejoji.[4] An kaddamar da shirin African American Studies dangane da kokarinta.[4]
Kuma tana cikin wadanda suka samar da "Acholonu Research Center" don bin diddigin tarihin Nahiyar Afurka, wanda ya zamo bincike na farko da aka sanya wa sunan mace a Najeriya.[4][6]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Catherine ta fito takarar shugaban kasan Najeriya a zaben shekara ta (1992) a karkashin jam'iyyar National Republican Convention inda daga bisani bataci nasara ba.[3][7] A wannan lokaci kuma mijinta shine mataimakin gwmanan jihar Imo daga jam'iyya daya.[7][8]
Ayyuka da Karramawa
[gyara sashe | gyara masomin]Rubutu
[gyara sashe | gyara masomin]Catherine tayi fice a fannin salon magana a Najeriya, daga cikin ayyukanta sun hada da Heinemann Book of African Female Writers da dai sauransu.[6] Ana la'akari da littafin Afro-Surrealist matuka.[6][9][10][11][12]
Littafin "Western and Indigenous Traditions in Modern Igbo Literature"
[gyara sashe | gyara masomin]Littafi ne da aka gyara daga binciken da tayi a yayin karatun digirin ta na uku wanda Dusseldorf University Press suka wallafa, wanda ya wanzu a jami'oin kasar Germany. Chidi T. Maduka, ya suki aikin da cewa bai da inganci sosai saboda baiyi wani gamsasshen bayani akan rubuce-rubucen Igbo ba, don haka aka soke aikin da cewa ya rasa cikakken bayanai. Har wayau, an sama karancin bayani kan malamai da kuma munanan tawaya.[13]
The Igbo Roots of Olaudah Equiano
[gyara sashe | gyara masomin]Littafin ta na farko da tayi bayanin asalin harshen Igbo dangane da tarihin Olaudah Equiano a Isseke, Ihiala.[6][14] Har wayau, masana tarihi sun soki aikin sosai musamman ta fuskan salon tarihin da ta ayyana a kundin.[5][15][16]
A wani nazarin, an soki labarin a matsayin tarihin gizo, da karerayi dangane da tarihin iyalan Equiano.[17] A wani nazari na Research in African Literatures, Paul Edwards yayi watsi da aikin gaba daya inda yayi ikirarin cewa bai kai ingancin binciken karatun jami'a ba.[18] Ode Ogede shima ya soki aikin sosai inda ya bayyana cewa wanna daya daga cikin misalan yadda ake canza asalin tarihi don cimma wani buri na daban, ba tare da wani sila na binciken ilimi ba kuma ya nemeta da tayi watsi da sabbin bayanin kan asalin Olaudah Equiano.[19]
Christopher Fyfe yayin nazari akan International Journal of African Historical Studies, ya nuna cewa aikinta gudunmawa ne sosai akan ainihin tarihin mutanen Afurka amma duk da haka ya jawo hankali kan suka Edward yayi wa aikin.[20] Erving Beauregard daga jami'ar University of Dayton, ya nuna cewa aiki ne mai kayatarwa sannan ya jinjina mata akan tarihin musamman na kusan shekaru 200 da suka shude.[21][22]
Duk da haka, Catherine tayi watsi da soke-soken inda ta nuna cewa kawai suka ne na adawa.[6][23]
Littafin Motherism : The Afrocentric Alternative to Feminism
[gyara sashe | gyara masomin]Aiki ne da ya samo asali daga binciken ta na jami'a wanda ya zamo fitaccen aiki akan nazarin jinsi a Afurka. Kuma ya jawo cigaba a fannin ilimin haihuwa a kasashen Turawa.
Sauran ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Abotan ta da Al Gore ne yasa har ta rubuta littafi The Earth Unchained: A Quantum Leap in Consciousness: don maida martani ga Al Gore akan sake binciko tarihin asalin Afurka da ya bace da kuma danganta shi wajen magance matsalolin duniya. Catherine tayi ikirarin cewa ta sama bayanai ta hanyar wahayi daga ubangiji, kuma ta kwashe tsawon kwanaki 14 tana rubutawa.[6]
Littafin ta na They Lived Before Adam: Pre-Historic Origins of the Igbo ya lashe lambar yabo na "Flora Nwapa Award for Literary Excellence" da kuma "Philis Wheatley Book Award" a taron Harlem Book Fair, na shekara ta 2009. Littafin The Gram Code of African Adam: Stone Books and Cave Libraries, Reconstructing 450,000 Years of Africa's Lost Civilizations wanda yayi bayani kan tsaffin duwatsun Ikom monoliths, wanda tayi ikirarin cewa yayi sanadiyar salon rubuta a zamunan Afurka na baya. Sannan kuma malamai kadan suka duba littafin ba kafin a wallafa shi.[24]
Kuma sannan ba'a san ayyukan ba sosai a kasashen waje.[5]
Ra'ayi
[gyara sashe | gyara masomin]Catherine tana da ra'ayin zamantakewa na dawainiya da juna kuma tana adawa da ra'ayin 'yancin mata (feminism).[6][25] Bata yarda da ra'ayin makarantun Alice Walker, Buchi Emecheta, Flora Nwapa da sauran makarantun da suke da ra'ayi akan 'yancin mata, tare da sukan su da bata tarbiya ta hanya halarta madugo da sauran al'adu wanda basu da alaka da ainihin al'adun matan Afurka.[6][26][27] Ta nuna cewa tattalin arziki bane ke jawo martaba a Afurka amma ba jinsi ba.[26][28] Haka zailka ra'ayinta na uwantaka "mothernism", na haihuwa da raino - na jawo hankali akan haihuwa da raino da mata ke yi, kuma yana bunkasa biyayya ga maza ba wai gaba da gaba da maza ba da sunan taimakekeniya tsakanin maza da mata ba.[26][29][30] Wannan ra'ayi nata ya samu murtani daga kungiyar matan feminism na zamani.[31][32]
Catherine ta nuna kawo addinin musulunci a matsayin mulkin mallaka, wanda ya jawo watsewar tsarukan mulkin Afurka kuma ya rage armashin rayuwa ga mata.[26]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Catherine ta mutu a ranar( 18 ) ga watan Mayu a shekara ta (2014) daga cutar koda a lokacin tana da shekaru (62).[33]
Martaba
[gyara sashe | gyara masomin]National Council of Women Societies (NCWS) ta lissafo ta acikin matan Najeriya da suka sama daukaka a shekara ta (2017).[34] An zabi littattafan ta a wajen karatun makarantun sakandare da jami'oi na Najeriya, da kuma wajen nazarin al'adun Afurka a sassan jami'oin kasashen Amurka da kuma Turai.[34]
Bibilyo
[gyara sashe | gyara masomin]Wakoki
[gyara sashe | gyara masomin]- "Going Home"
- "Spring's Last Drop"
- "Dissidents"
- "Harvest of War"
- "Other Forms of Slaughter"
- Collections
- The Spring's Last Drop, 1985
- Nigeria in the Year 1999, 1985
- Recite and Learn – Poems for Junior Primary Schools, 1986
- Recite and Learn – Poems for Senior Primary Schools, 1986
Wasanni da Drama
[gyara sashe | gyara masomin]- Trial of the Beautiful Ones: a play in one act, Owerri, Nigeria: Totan, 1985—based on the Igbo ogbanje myth.[35]
- The Deal and Who is the Head of State, Owerri, Nigeria: Totan, 1986[36]
- Into the Heart of Biafra: a play in three acts, Owerri, Nigeria: C. Acholonu, 1970[37]
Kasidu da kuma Labaran Gaskia
[gyara sashe | gyara masomin]- Western and Indigenous Traditions in Modern Igbo Literature , 1985.
- Motherism, The Afrocentric Alternative to Feminism, 1995.
- The Igbo Roots of Olaudah Equiano, 1995, revised 2007.
- The Earth Unchained: A Quantum Leap in Consciousness: a reply to Al Gore, 1995
- Africa the New Frontier – Towards a Truly Global Literary Theory for the 21st Century. Lecture Delivered to the Association of Nigerian Authors annual Convention, 2002.
- The Gram Code of African Adam: Stone Books and Cave Libraries, Reconstructing 450,000 Years of Africa's Lost Civilizations, 2005
- They Lived Before Adam: Pre-Historic Origins of the Igbo – The Never-Been-Ruled (Ndi Igbo since 1.6 million B.C.), 2009. Winner of the USA-based International Book Awards (2009) in the Multi-cultural non-fiction category.
- The Lost Testament of the Ancestors of Adam: Unearthing Heliopolis/Igbo Ukwu – The Celestial City of the Gods of Egypt and India, 2010
- Eden in Sumer on the Niger: Archaeological, Linguistic, and Genetic Evidence of 450,000 Years of Atlantis, Eden and Sumer in West Africa, 2014
Littattafai da ta wallafa
[gyara sashe | gyara masomin]- The Igbo Roots of Olaudah Equiano: An Anthropological Research Jan 1, 1989[38]
- The Deal and Who is the Head of State[38]
- The Spring's Last Drop[38]
- Nigeria in the year 1999 (TOT Series)
- Into the Heart of Biafra (TOP Series)
- Trial of the Beautiful Ones[38]
Babin Mukalai
[gyara sashe | gyara masomin]- (with Joyce Ann Penfield), "Linguistic Processes of Lexical Innovation in Igbo." Anthropological Linguistics. 22 (1980). 118–130.
- "The Role of Nigerian Dancers in Drama." Nigeria Magazine. 53.1 (1985). 33–39.[36]
- "The Home of Olaudah Equiano – A Linguistic and Anthropological Research", The Journal of Commonwealth Literature. 22.1 (1987). 5–16.[39]
- "L'Igbo Langue Litteraire: Le Cas du Nigeria." [Literary Igbo Language: The Case of Nigeria.] Notre Librairie: Revue du Livre: Afrique, Caraibes, Ocean Indien. 98 (Jul–Sept 1989). 26–30.
- "Mother was a Great Man." In The Heinemann Book of African Women's Writing. Ed. Charlotte H. Bruner. London: Heinemann, 1993. 7–14.
- "Motherism: The Afrocentric Alternative to Feminism." Ishmael Reed's Konch Magazine. (March–April 2002).
- [40]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Umeh, Marie (2011). "Acholonu, Catherine Obianuju". Oxford African American Studies Center. doi:10.1093/acref/9780195301731.013.48143. ISBN 9780195301731. Retrieved 19 May 2021.
- ↑ 2.0 2.1 "Prof Catherine Obianuju Acholonu". faculty.ucr.edu. Retrieved 2020-05-30.
- ↑ 3.0 3.1 Uduma, Kalu (29 May 2020). "Celebrated scholar, Acholonu dies at 63". Vanguard Media Limited. Retrieved 19 March 2014.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 4.5 Akyeampong, Emmanuel Kwaku; Gates, Henry Louis (2 February 2012). Dictionary of African Biography. OUP USA. pp. 85–86. ISBN 978-0-19-538207-5.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 5.3 Owomoyela, Oyekan (2008). The Columbia Guide to West African Literature in English Since 1945. Columbia University Press. pp. 56–57. doi:10.7312/owom12686. ISBN 9780231126861. JSTOR 10.7312/owom12686
- ↑ 6.00 6.01 6.02 6.03 6.04 6.05 6.06 6.07 6.08 6.09 Otiono, Nduka (29 May 2020). "Catherine Acholonu (1951-2014) The Female Writer as a Goddess"(PDF). Nokoko. 4: 67–89 – via Institute of African Studies.
- ↑ 7.0 7.1 Chuku, Gloria (2009). "Igbo Women and Political Participation in Nigeria, 1800s-2005". The International Journal of African Historical Studies. 42 (1): 81–103. ISSN 0361-7882. JSTOR 40282431
- ↑ Osinulu, Clara (1996). Nigerian women in politics, 1986-1993 /. Ikeja, Lagos State, Nigeria. hdl:2027/uva.x006029213
- ↑ Ohaeto, Ezenwa (1988-01-01). "The Other Voices: The Poetry of Three Nigerian Female Writers". Canadian Journal of African Studies. 22 (3): 662–668. doi:10.1080/00083968.1988.10804235. ISSN 0008-3968.
- ↑ Ogede, Ode S. (1999-01-01). "Exile and the Female Imagination; The Nigerian Civil War, Western Ideology (Feminism), and the Poetry of Catherine Acholonu". Neohelicon (in Turanci). 26 (1): 125–134. doi:10.1023/A:1010991907116. ISSN 1588-2810. S2CID 162054849.
- ↑ Raji–Oyelade, Aderemi (2006-06-01). "Representational Exposures: The Album of Nigerian Women's Poetry (1985–2006)". Matatu (in Turanci). 33 (1): 293–316. doi:10.1163/18757421-033001035. ISSN 1875-7421.
- ↑ Nwachukwu-Agbada, J. O. J. (1986). "Review of The Spring's Last Drop". World Literature Today. 60 (3): 510. doi:10.2307/40142399. ISSN 0196-3570. JSTOR 40142399.
- ↑ Maduka, Chidi (1989). "Review of Western and Indigenous Traditions in Modern Igbo Literature". Research in African Literatures. 20 (1): 116–119. ISSN 0034-5210. JSTOR 3819093
- ↑ M'Baye, Babacar (11 February 2010). The Trickster Comes West: Pan-African Influence in Early Black Diasporan Narratives. Univ. Press of Mississippi. p. 108. ISBN 978-1-60473-352-5.
- ↑ Law, Robin (December 2002). "Individualising the Atlantic Slave Trade: The Biography of Mahommah Gardo Baquaqua of Djougou (1854)". Transactions of the Royal Historical Society. 12: 113–140. doi:10.1017/S008044010200004X. ISSN 0080-4401. S2CID 166059537
- ↑ Rolingher, Louise (1 January 2004). "A Metaphor for Freedom: Olaudah Equiano and Slavery in Africa". Canadian Journal of African Studies. 38 (1): 88–122. doi:10.1080/00083968.2004.10751282. ISSN 0008-3968. S2CID 142600256
- ↑ Isichei, Elizabeth (March 1992). "The Life of Olaudah Equiano, or Gustavus Vassa the African. Edited by Paul Edwards. (Revised edition). Basingstoke and London: Longman, 1989. Pp. xxxviii+186. £4.50 (paperback). - The Igbo Roots of Olaudah Equiano. By Catherine Obianuju Acholonu. Owerri, Nigeria: Ata Publications, 1989. Pp. viii+184. No price given". The Journal of African History. 33 (1): 164–165. doi:10.1017/S0021853700032084. ISSN 1469-5138
- ↑ Edwards, Paul (1990). "Review of The Igbo Roots of Olaudah Equiano". Research in African Literatures. 21 (2): 124–128. ISSN 0034-5210. JSTOR 3819289
- ↑ Ogede, O. S. (1991). "Review of The Igbo Roots of Olaudah Equiano". Africa: Journal of the International African Institute. 61 (1): 138–141. doi:10.2307/1160281. ISSN 0001-9720. JSTOR 1160281. S2CID 144195302
- ↑ Fyfe, Christopher (1990). "Review of The Igbo Roots of Olaudah Equiano". The International Journal of African Historical Studies. 23 (4): 744–745. doi:10.2307/219537. ISSN 0361-7882. JSTOR 219537
- ↑ "Book reviews". The African Book Publishing Record. 18 (1): 9. 1 January 1992. doi:10.1515/abpr.1992.18.1.7. ISSN 0306-0322.
- ↑ Sabino, Robin; Hall, Jennifer (1 March 1999). "The Path Not Taken: Cultural Identity in the Interesting Life of Olaudah Equiano". MELUS. 24 (1): 5–19. doi:10.2307/467904. ISSN 0163-755X. JSTOR 467904
- ↑ Carretta, Vincent (3 December 2009). "Olaudah Equiano and the Igbo World: History, Society, and Atlantic Diaspora Connections (review)". Research in African Literatures. 40 (4): 183–184. doi:10.2979/RAL.2009.40.4.183. ISSN 1527-2044
- ↑ Lombaard, Christoffel (8 February 2017). "Mystifying moments in Bible interpretation: An exploration of some implied backgrounds to three kinds of unusual Bible readings". HTS Teologiese Studies / Theological Studies. 73 (3): 8. doi:10.4102/hts.v73i3.3495. ISSN 2072-8050
- ↑ Phillips, Layli (19 September 2006). The Womanist Reader: The First Quarter Century of Womanist Thought. Routledge. p. 41. ISBN 978-1-135-91974-0.
- ↑ 26.0 26.1 26.2 26.3 Edwin, Shirin (2016). "Connecting Vocabularies". Connecting Vocabularies:: A Grammar of Histories, Politics, and Priorities in African and Islamic Feminisms. Privately Empowered. Expressing Feminism in Islam in Northern Nigerian Fiction. Northwestern University Press. pp. 35–76. ISBN 978-0-8101-3368-6. JSTOR j.ctt22727xh.7
- ↑ "The making of a gendered nation in postcolonial West African video, film, and literatures - ProQuest": 182. ProQuest 304707802
- ↑ "African Women as Victims or Heroines?: Obiwuruotu Women's Music, Gender, Marriage, and Culture among the Igbo in Nigeria - ProQuest": 15. ProQuest 1984625281
- ↑ Etim, Eyoh (1 January 2020). Nyambi, Oliver (ed.). ""Herstory" versus "history": A motherist rememory in Akachi Ezeigbo's The Last of the Strong Ones and Chimamanda Adichie's Half of a Yellow Sun". Cogent Arts & Humanities. 7 (1): 1728999. doi:10.1080/23311983.2020.1728999
- ↑ Korieh, Chima J.; Okeke-Ihejirika, Philomina E. (19 November 2008). Gendering Global Transformations: Gender, Culture, Race, and Identity. Routledge. p. 114. ISBN 978-1-135-89385-9.
- ↑ Azuah, Unoma N. (1 June 2005). "The Emerging Lesbian Voice in Nigerian Feminist Literature". Matatu. 29–30 (1): 129–142. doi:10.1163/18757421-029030009. ISSN 1875-7421
- ↑ Umer, Marie Linton (26 April 1997). "Children's Literature in Nigeria Revolutionary Omissions". Matatu. 17–18 (1): 191–206. doi:10.1163/18757421-90000224. ISSN 1875-7421
- ↑ "Nigeria: Celebrated Scholar, Acholonu Dies At 63". allAfrica.com. 19 March 2014. Retrieved 19 March 2014.
- ↑ 34.0 34.1 "Catherine Obianuju Acholonu (1951-2014) - ProQuest". ProQuest 1518976685
- ↑ Boyce-Davies, Carole; Ogundipe-Leslie, Molara (February 1995). Moving Beyond Boundaries (Vol. 1): International Dimensions of Black Women's Writing (in Turanci). NYU Press. p. 237. ISBN 978-0-8147-1238-2.
- ↑ 36.0 36.1 "Catherine Obianuju Acholonu: Works". www.postcolonialweb.org. Retrieved 2020-05-29.
- ↑ Acholonu, Catherine Obianuju. Into the heart of Biafra: a play in three acts (in Turanci). Owerri, Nigeria: C. Acholonu. OCLC 17473309.
- ↑ 38.0 38.1 38.2 38.3 "Catherine Obianuju Acholonu". www.amazon.com (in Turanci). Retrieved 2021-05-19.
- ↑ Obianju Acholonu, Catherine (1987-03-01). "The Home of Olaudah Equiano - a Linguistic and Anthropological Search". The Journal of Commonwealth Literature (in Turanci). 22 (1): 5–16. doi:10.1177/002198948702200102. ISSN 0021-9894.
- ↑ Acholonu, Catherine Obianuju (1986). "Review of Critical Perspectives on Christopher Okigbo". Research in African Literatures. 17 (4): 613–614. ISSN 0034-5210. JSTOR 3819536.