Chioma Ubogagu
Chioma Ubogagu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Landan, 10 Satumba 1992 (32 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Tarayyar Amurka Birtaniya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Makaranta | Coppell High School (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 1.7 m |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Chioma Grace Ubogagu (an haife ta ne a 10 ga watan Satumban, a shekara ta alif 1992A.C) ta kasan ce kuma ƙwararriyar 'yar wasan ƙwallon ƙafa ce wadda take taka leda a matsayin 'yar wasan gaba na Real Madrid CF a cikin Spanish Primera División . Ta taba taka leda a Orlando Pride, Brisbane Roar, Houston Dash da Arsenal . Ubogagu ta buga wasan kwallon kafa na jami'ar Stanford kuma ta buga wasanni a lokacin da take matashiya a matakai daban-daban a Amurka, inda ta lashe Kofin Duniya na mata na U-20 a shekarar 2012 .
Tarihin Rayuwa da Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Ubogagu an haife ta ne a Landan, inda iyayenta suke da zama, mahaifiyar ta Tina ma'aikaciyar jinya ce shi kuma mahaifinta Aloy ma'aikacin zamantakewar al'umma, dukkanin su 'yan Najeriya ne da suka ƙaura Landan don neman damar aiki. Tun tana shekara 3, iyayenta suka rabu inda hakan yass ta ƙaura tare da mahaifiyarta da babban yayanta zuwa Coppell, Texas a wani yanki a cikin Dallas – Fort Worth metroplex inda a nan ne ta fara harkar kwallon kafa bayan ta shiga kungiyar ƙwallon ƙafa ta D'Feeters.
Kungiyoyin da tayi Wasa
[gyara sashe | gyara masomin]'Arsenal Ladies, 2015
[gyara sashe | gyara masomin]Houston Dash, 2016
[gyara sashe | gyara masomin]Orlando Pride, 2017–2019
[gyara sashe | gyara masomin]Loan at Brisbane Roar
[gyara sashe | gyara masomin]CD Tacón / Real Madrid, 2019 – yanzu
[gyara sashe | gyara masomin]Wasanta a Mataki na Duniya
[gyara sashe | gyara masomin]Saboda iyayenta da wurin haihuwarta, Ubogagu ta na da damar wakiltar Najeriya, Ingila ko Amurka. Ta zaɓi wakiltar Amurka a mataki na yarinta, inda ta bugawa ƙasar wasanni a mataki na 'yan ƙasa da shekaru 18, 20 kuma 23. A mataki na manyan 'yan wasa kuwa sai ta zaɓi wakiltar Ingila, ta hanyar karɓar tayin da aka mata a Oktoban 2018 kuma ta fara zama babbar fitacciya ƙasar Ingila ɗin ne a ranar 8 Nuwamban 2018.
'Yan Uwa da Dangi
[gyara sashe | gyara masomin]Kakanta Austin Eneuke ya buga wa Najeriya da Tottenham Hotspur wasa . Ubogagu ta kasance masoyiyar Arsenal a duk sanda suke kallon wasan Arewacin London, duk da mahaifinta ya so rinjayarta da ta goyi bayan Tottenham.
Ƙididdigar Wasanni
[gyara sashe | gyara masomin]Kulab
[gyara sashe | gyara masomin]Kulab | Lokaci | League | Kofi | Nahiya | Jimla | |||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rabuwa | Ayyuka | Goals | Ayyuka | Goals | Ayyuka | Goals | Ayyuka | Goals | ||
Arsenal | 2015 | FA WSL 1 | 14 | 6 | 5 | 1 | - | - | 19 | 7 |
Houston Dash | 2016 | NWSL | 15 | 1 | - | - | - | - | 15 | 1 |
Orlando Pride | 2017 | NWSL | 20 | 4 | - | - | - | - | 20 | 4 |
2018 | 21 | 4 | - | - | - | - | 21 | 4 | ||
2019 | 17 | 4 | - | - | - | - | 17 | 4 | ||
Jimla | 58 | 12 | 0 | 0 | 0 | 0 | 58 | 12 | ||
Brisbane Roar (rance) | 2018–19 | W-League | 11 | 2 | - | - | - | - | 11 | 2 |
Jimlar aiki | 98 | 21 | 5 | 1 | 0 | 0 | 103 | 22 |
Nasorinta a duniya
[gyara sashe | gyara masomin]A'a | Kwanan wata | Wuri | Kishiya | Ci | Sakamakon | Gasa | Ref. |
---|---|---|---|---|---|---|---|
1 | 8 Nuwamba 2018 | BSFZ-Arena, Maria Enzersdorf, Ostiriya | Samfuri:Country data AUT</img>Samfuri:Country data AUT | 1 - 0 | 3-0 | Abokai |
Lambobin Yabo
[gyara sashe | gyara masomin]Ingila
- SheBelieves Cup : 2019
Bayanan kula
[gyara sashe | gyara masomin]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]
Hanyoyin haɗin waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Chioma Ubogagu – FIFA competition record
- Bayanin Stanford Archived 2016-03-04 at the Wayback Machine
- Bayanin Kwallon Amurka
- Bayanin Arsenal
- Chioma Ubogagu at Soccerway
- Mukaloli marasa hujja
- Webarchive template wayback links
- Mutanen Najeriya
- 'Yan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Ingila
- Yan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya
- Yan wasan kwallon kafan American daga Texas
- Mata yan wasan ƙwallon ƙafa
- Mutanen Afirka
- Mazauna Turai
- Haifaffun 1992
- Bakaken fata na ingila
- Shahararrun mata a kwallon kafa