Cynthia Akuetteh
Cynthia Akuetteh | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1948 (75/76 shekaru) |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Ƙabila | Afirkawan Amurka |
Karatu | |
Makaranta |
Long Island University (en) School of International and Public Affairs, Columbia University (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya |
Cynthia Akuetteh (an haifi Cynthia Helen Archie a shekara ta 1948)[1] jami'ar diflomasiyya ce kuma ta kasance Jakadiyar Amurka a São Tomé da Principe kuma jakadar Amurka a ƙasar Gabon.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Akuetteh Cynthia Helen Archie a birnin Washington, DC ga Richard Louis Archie II da Sallie Dolores Hines.[2] Ta sami digiri na BA a fannin tarihi, tare da samun karramawa daga CW Post College na Jami'ar Long Island a 1970, kuma an ba ta digiri na biyu a (National Security Resource Policy) daga Jami'ar Tsaro ta Kasa a 1973. Akuetteh ta kammala karatun digiri na shekaru biyu a Jami'ar Columbia. [3]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Akuetteh ta fara aiki tare da Peace Corps. Aikinta na farko shine Jami'ar Shirye-shirye a Washington, DC Daga nan ta koma Ghana a matsayin mataimakiyar Daraktar shirin a can. Bayan Akuetteh ta shiga ma'aikatar harkokin wajen Amurka a shekarar 1984, ta gudanar da ayyuka da dama na ƙasa da ƙasa a ƙasashen; Nijar, Tanzania, Canada da Venezuela . Yawancin ayyukanta na baya sun mayar da hankali kan nahiyar Afirka. Ta yi aiki a matsayin mataimakiyar darakta mai kula da manufofin tattalin arziki na ofishin Afirka, sannan ta zama daraktar ofishin kula da harkokin Afirka ta tsakiya, inda ta riƙa kula da hulɗar dake tsakanin ƙasashen biyu da ƙasashe goma na Afirka. Ta kuma kasance mataimakiyar sakataren harkokin Afirka daga shekara ta 2012 zuwa 2013. [4] A shekara ta 2012 ta jagoranci tawagar Amurka zuwa wani taron Hukumar Kula da Yankin Neja-Delta da Ƙungiyar Cigaban Ƙasa da aka gudanar a Fatakwal. [5]
Ta bayyana a gaban kwamitin kula da harkokin ƙasashen waje na majalisar dattijai a ranar 17 ga watan Disamba, 2013 don tattaunawa kan manufarta game da matsayinta na jakada. Bayan majalisar dattawa ta amince mata, an rantsar da ita a matsayin jakadiyar Amurka a Jamhuriyar Gabon da São Tomé and Principe a ranar 1 ga Agusta, 2014. Ta gabatar da takardun shaidarta a waɗannan ƙasashe a ranar 26 ga Disamba, 2014, da Afrilu 10, 2015.[6][7] A lokacin da ake tashe tashen hankula a Gabon, ta bayyana damuwarta a bainar jama'a game da duk wani yunƙuri na "ƙarin tsarin mulki" na sauyin mulki. da kuma inganta hanyoyin "dimokradiyya". [8]
A watan Mayun 2015, Akuetteh ta yi maraba da sojojin Amurka da suka shiga tare da sojoji daga ƙasashen Afirka 15 da kuma MDD a bikin buɗe yarjejeniyar-(Central Accord 2015 exercise) a Libreville, Gabon. Akuetteh ta bayyana cewa, babban maƙasudin gudanar da wannan aiki shi ne wanzar da zaman lafiya da ƙarfafa alaƙar ƙasashen da ke halartar taron. [9] Ta yi ritaya a ranar 26 ga watan Fabrairu, 2018.
Rayuwar ƙashin kanta
[gyara sashe | gyara masomin]Akuetteh ta taɓa auren Nii Akuetteh, wanda ya kafa Cibiyar Nazarin Dimokuradiyya da Rikici a Ghana.[10] Suna da yara biyu manya.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]Wikimedia Commons on Cynthia Akuetteh
- ↑ "Cynthia Helen Akuetteh (1948- ) •" (in Turanci). 2015-06-01. Retrieved 2023-03-07.
- ↑ Akuetteh, Cynthia Helen Black Past, accessed March 7, 2016
- ↑ Cynthia Akuetteh: Global Business Forum Baylor University,March 2013
- ↑ Cynthia Akuetteh U.S. Department of State, accessed March 7, 2016
- ↑ US – Nigeria Bi-national Commission meeting begins in Port Harcourt Channel S TV, Oct 16, 2012
- ↑ L’ambassadrice des Etats-Unis, Cynthia Akuetteh tombe sous le charme de Franceville Times Gabon, November 14, 2015
- ↑ "Cynthia Helen Akuetteh (1948–)". Department of State.
- ↑ US opposes 'coup' in Gabon; opposition mounts against Bongo The News Nigeria, January 13, 2015
- ↑ US military kicks off training exercise with African and European partners Defense Media, May 13, 2015
- ↑ "Cynthia Helen Akuetteh (1948- ) •" (in Turanci). 2015-06-01. Retrieved 2023-03-07.
Diplomatic posts | ||
---|---|---|
Magabata Eric D. Benjaminson |
United States Ambassador to Gabon 2014–2018 |
Magaji Joel Danies |
United States Ambassador to Sao Tome and Principe 2015–2018 |