Dennis Idahosa
Dennis Idahosa | |||||
---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - District: Ovia North East/Ovia South West
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Ovia ta Kudu maso Yamma, 8 Nuwamba, 1980 (44 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Harshen uwa | Harshen Edo | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Harshen Edo Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Mamba | Majalisar Dokokin Najeriya ta 10 | ||||
Imani | |||||
Addini | Kiristanci | ||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Dennis Idahosa (an haife shi a ranar 11 ga watan Agusta 1980) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin gwamnan jihar Edo tun a ranar 12 ga watan Nuwamba 2024. Ya taɓa zama ɗan majalisar wakilan Najeriya daga shekarun 2019 zuwa 2024. [1]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Dennis Idahosa a ranar 11 ga watan Agusta 1980, [2] a garin Benin, Jihar Edo. [1] Ya yi karatun digiri a fannin zamantakewa da kuma digiri na biyu a fannin shari'a a Kanada da Najeriya. [3]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Ya yi aiki a fannin kiwon lafiya na kamfanoni masu zaman kansu da kuma sassan kawance kafin shiga siyasa. An naɗa shi kwamishinan ma’aikatar zuba jari ta jihar Edo, haɗin gwiwar jama’a da masu zaman kansu (2014-2015) ta gwamnatin Adams Oshiomhole. Ya kasance memba na Hukumar National Green Wall, Abuja, daga watan Maris 2018 zuwa Nuwamba 2018. [3]
A shekarar 2019, an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai kuma ya sake zaɓe a shekarar 2023 a karo na biyu a ofis inda ya doke Omosede Igbinedion. [4]
A ranar 22 ga watan Satumba 2024, aka ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen mataimakin gwamna a zaɓen gwamna.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nass.gov.ng. Retrieved 2024-03-01. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ Ogbankwa, Douglas (11 August 2024). "44 Hearty Cheers to Right Honourable Dennis Idahosa: An Icon Whose Mantra is "Leadership is Responsibility"". Nigerian NewsLeader. Retrieved 3 October 2024.
As you celebrate your 44th birthday today, sir, we honour you for all that you stand for. We celebrate your resilience, your resoluteness, and your astuteness.
- ↑ 3.0 3.1 "Dennis Idahosa: Steadily Climbing the Political Ladder". www.thisdaylive.com (in Turanci). Retrieved 2024-03-01. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":1" defined multiple times with different content - ↑ Nseyen, Nsikak (2023-09-09). "Tribunal dismisses PDP, LP Petitions, upholds Dennis Idahosa's victory in Edo". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-03-01.