Diamond Zahra

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Diamond Zahra
Rayuwa
Haihuwa Maradi, 25 ga Maris, 1996 (28 shekaru)
ƙasa Nijar
Karatu
Harsuna Faransanci
Hausa
Turanci
Sana'a
Sana'a Jarumi da filmmaker (en) Fassara

Zahra Muhammad wacce aka fi sani da Diamond Zahra ko Zahra Buzuwa ƙwararriyar yar wasan kwaikwayo ce 'yar Nijar. An haifi Zahra a garin Tahoua amma ta yi karatun firamare da sakandare a Maraɗi duk a Jamhuriyar Nijar. Ta fito daga ƙabilar Abzinawa.[1]

Rayuwar farko da aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Zahra ta koma Najeriya domin shiga masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood a shekarar 2018. Fim ɗin da yasa jarumar ta shahara shi ne fim ɗin "Zuma Da Maɗaci (2018). Zarah ta fito a fina-finan Hausa daban-daban kamar su Hanan, Barrister Kabeer, Gidan Sirikai, Sirrin So (Series), Yaudara, da dai sauransu. Ta kuma fito a cikin waƙoƙin Hausa da dama tare da mawaƙan Hausa kamar; Hamisu Breaker, Garzali Miko, Umar M Shariff da sauransu.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]