Farooq Kperogi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Farooq Kperogi
Rayuwa
Haihuwa Baruten, 30 ga Maris, 1973 (51 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Georgia State University (en) Fassara
University of Louisiana at Lafayette (en) Fassara
Jami'ar Bayero
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a linguist (en) Fassara, Malami da ɗan jarida
farooqkperogi.com

Farooq Adamu Kperogi (An haifeshi ranar 30 ga watan Maris din Shekarar 1973) tshohon ɗan jarida ne kuma malamin ilimin hanyoyin sadarwa na zamani a kasar Amurka. Farooq yayi aikin jarida a gidaje jaridun Najeriya kamar Daily Trust da kuma tsohuwar jaridar New Nigerian ta gwamnatin tarayya da kuma Daily Triumph.[1]

Kperogi yana cikin masu rubuta jawabin shugaban kasa a zamanin mulkin Obasanjo, kuma ya koyar da aikin jarida a Jami'ar Ahmadu Bello da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna. Yana koyar da aikin jarida a Jami'ar Jihar Kennesaw da ke Jojiya, Amurka.[2][3][4] Shi ne kuma marubucin (Glocal English: The Changing Face and Forms of Nigerian English), wanda aka buga a cikin shekara ta 2015, a matsayin juzu'i na 96 a cikin jerin Insights na Berkeley a cikin Linguistics da Semiotic.[5][6]

Rayuwar farkon da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Kperogi a shekara ta 1973, a Okuta, karamar hukumar Baruten a jihar Kwara, Najeriya.[7] Ya halarci Jami'ar Bayero tsakanin 1993 zuwa 1997, inda ya samu digiri na farko a fannin sadarwa. Ya sami digiri na biyu a fannin sadarwa a Jami'ar Louisiana ta Lafayette da kuma Ph.D. daga Jami'ar Jihar Jojiya a Amurka a shekara ta 2011.[2]

Bayan nan da Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan kammala karatunsa a Jami'ar Bayero ta Kano, Kperogi ya fara aikin jarida a Katsina da Kano a matsayin mai kawo rahotanni, kafin ya koma Media Trust a matsayin wakilin rusasshiyar jaridar Weekly Trust. Ya kuma yi aiki da rusasshiyar jarida mallakar gwamnatin tarayya, wato jaridar New Nigerian, a farkon shekarun 2000. Kperogi ya fara aikin sa ne a tsakanin shekarar 2000 zuwa 2002 a Kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, inda ya koyar da aikin jarida da sadarwa-(journalism and mass communication). Ya kuma koyar a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya na ɗan wani lokaci a shekarar 2004.[3] A tsakanin 2002 zuwa 2004, Kperogi ya yi aiki a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo a matsayin marubucin jawabin shugaban kasa kuma mai bincike. Kperogi ya rubuta ginshiƙai biyu, “Politics of Grammar" da “Notes from Atlanta”, don bugawa a jaridar Daily Trust.

Politics of Grammar[gyara sashe | gyara masomin]

Kperogi ya yi rubutu da yawa game da Turancin Najeriya.[8]

Notes from Atlanta[gyara sashe | gyara masomin]

Aikin da aka wallafa[gyara sashe | gyara masomin]

  • Glocal English: The Changing Face and Form of Nigerian English in Global World. New York: Peter Lang, 2015. 08033994793.ABA

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kperogi: The Man Who Redefined Grammar Column Writing in Nigeria". jarushub.com. JarusHub. Archived from the original on 6 October 2017. Retrieved 23 March 2018.
  2. 2.0 2.1 "About me". farooqkperogi.com. Farooq A. Kperogi. Retrieved 6 October 2017.
  3. 3.0 3.1 "Farooq Kperogi". socm.hss.kennesaw.edu. Kennesaw State University. Retrieved 6 October 2017.
  4. "Why British English is full of silly-sounding words". bbc.com. British Broadcasting Corporation. Retrieved 6 October 2017.
  5. "Berkeley Insights in Linguistics and Semiotics". www.peterlang.com. Peter Lang. Retrieved 6 October 2017.
  6. "7 Questions to a Linguist: Dr. Farooq Kperogi on "Glocal" English". altalang.com. ALTA. Archived from the original on 6 October 2017. Retrieved 6 October 2017.
  7. "Kperogi: The Man Who Redefined Grammar Column Writing in Nigeria". jarushub.com. JarusHub. Archived from the original on 6 October 2017. Retrieved 6 October 2017.
  8. Christine Ro (19 June 2017). "Why British English is full of silly-sounding words". BBC. Retrieved 21 January 2018.