Farouk Lawan
Farouk Lawan | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
5 ga Yuni, 2007 - District: Shanono/Bagwai
3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007
29 Mayu 1999 - District: Shanono/Bagwai | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Shanono, 6 ga Yuli, 1962 (62 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | Jami'ar Bayero | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa da ɗan kasuwa | ||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Farouk Muhammad LawanFarouk Lawan (Taimako·bayani) ( an haife shi a watan yuli a cikin shekara ta alif ɗari tara da sittin da biyu 1962) miladiyya, dan siyasar Najeriya ne wanda yayi dan majalisar wakilai ta taraiya sau huɗu daga shekara ta alif dari tara da casa'in da tara ( 1999 zuwa shekara ta dubu biyu da Sha biyar 2015), inda ya wakilci kananan hukumomin Bagwai da Shanono daga Jihar Kano.
Tarihin sa
[gyara sashe | gyara masomin]Lawan yayi karatu a Jami'ar Bayero dake Kano. Yayi aure yana da yaya hudu.[1]
Siyasar shi
[gyara sashe | gyara masomin]Farouk Lawal dan jam'iyar( PDP), ne kuma a cikin jam'iyyar ne ya lashe zaben dan majalisar wakilai har sau hudu (daga shekarar alif dari tara da casa'in da tara1999, izuwa shekarar 2011) Lawan ya rike muƙamin shugaban kwamitin kudi na majalisar lokacin tsohon kakakin majalisa Rt Hon Aminu Bello Masari.[2] Ya baiya na irin nasarar da ya samu tun awannan lokacin.[1]
Daga karshen shekara ta( 2007), an samu rikita rikitar cin hanci da rashawa da ta taso wadda yayi sanadiyyar murabus, wanda aka same shi dumu dumu ya karbi wasu kudi a hannun Patricia Etteh, Lawan ya karbi jagorancin kwamitin amintattu na majalisar. A yanzu wasu daga cikin yan siyasa na ganin lawan Farouk shi ya dace da ya tsaya takarar gwamnan jahar Kano.
Tsegumi kan tallafin mai
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Janairu shekara ta( 2012), Lawan yazama shugaban kwamitin bincike dangane da tallafin mai na Najeriya.[3] Kwamitin ne ya tayar da yan kasar akan ma'aikata su tafi yajin aiki domin nuna fushin su da janye tallafin mai wanda gwamnatin lokacin ta Goodluck Jonathan tayi.[4] Daga karshe kwamitin ya fitar da rahoton binciken sa a wannan dai shekarar, inda ya baiyana irin daruruwan miliyoyi na dala wanda gwamnatin kasar ke fitarwa ga kamfanonin mai na kasar da sunan tallafin mai.[5]
A watan Fabrairu shekarar (2013 ), an zargi Lawan da badakalar cinhanci bayan karbar kudin da sukakai ($500,000), daga hannun Femi Otedola, wani hamshakin dan kasuwar mai a Najeriya. Kudin wani bangare ne na cinhanci dala milayan uku $3m wanda Lawan din zai karba daga hannun dan kasuwar.[6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Honourable Farouk Lawan". National Assembly of Nigeria. Archived from the original on 2007-10-20. Retrieved 2012-07-04.
- ↑ Nwankwo, Chiawo (2007-11-01). "S'West Reps: Jostling for Etteh's seat". The Punch online. Archived from the original on 2007-11-01. Retrieved 2007-11-03.
- ↑ Nigeria’s President Jonathan ‘must act over fuel scam’, England: BBC News, 2012
- ↑ Nigerian fuel subsidy: Strike suspended, England: BBC News, 2012
- ↑ Nigeria’s President Jonathan ‘must act over fuel scam’, England: BBC News, 2012
- ↑ Nigeria anti-graft lawmaker charged with $3 mln bribe, United States: Reuters, 2013, archived from the original on 2014-02-12, retrieved 2020-03-07