Fatima Batul Mukhtar
Fatima Batul Mukhtar | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jahar Kano, 23 Mayu 1963 (61 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Bayero Jami'ar Ahmadu Bello |
Sana'a | |
Sana'a | botanist (en) da Malami |
Fatima Batul MukhtarFatima Batul Mukhtar (Taimako·bayani) wata malama ce a Najeriya, wacce farfesa ce a fannin Botany. Bincike-binciken nata ya ta'allaka ne kan "tsarin bunkasuwa, kimiyyar halittu, fasahar ƙere-kere da kuma kiyaye tsirrai". A shekarar, 2016, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta Mataimakiyar Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutse.[1]
Farkon rayuwa da Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Fatima acikin garin Kano a shekara ta 1963. Ta yi makarantar firamare ta Shahuchi da kuma makarantar firamare ta ka mata ta karatun firamare, sannan ta wuce kwalejin kwana lejin 'Yan Mata ta Gwamnati, da ke Dala a garin Kano domin karatun sakandaren ta. A shekarar ta 1984, ta samu digiri a fannin ilimin tsirrai a Jami’ar Ahmadu Bello . A shekar ta 1994, ta samu digirinta na biyu a Jami’ar Bayero . Ta kammala digirinta na uku a shekara ta 2005, wacce ta ƙware a fannin ilimin kimiyyar lissafi daga wannan jami'ar. A shekara ta 2012, ta shiga kwasa-kwasan ilimin kimiyyar kere-kere a Jami'ar Jihar Michigan . Tana daya daga cikin wadanda suka assasa masu kula da harkokin ilimi a jami'ar Northwest University Kano, kuma ta sance shugabar makarantar kimiyya ta farko a jami'ar. A shekarar 2015, ta zama mataimakiyar shugabar makarantar. A shekara ta 2016, an nada ta a matsayin mataimakiyar shugaban jami'ar Tarayya ta Dutse .
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "5 women who have made their marks in education". www.pulse.ng (in Turanci). 2018-03-08. Retrieved 2019-03-21.