Fatima Sana Shaikh (an haifeta ranar 11 ga watan Janairun, shekarar alif dubu ɗaya da Ɗari Tara da casa'in da biyu(1992))[1] 'yar fim ce ta ƙasar Indiya.[2] An san ta da ayyukanta a finafinan Hindi - yare, da talabijin. Fatima ta fito a matsayin yar zane-zane a fina-finai kamar Chachi 420 da kuma One 2 Ka 4.[3] Shekaru daga baya, ta buga Zoya a cikin fim ɗin Indiya na Tahaan wanda ya sami lambar yabo ta "The German Star of India" a bikin "Bollywood da Beyond" a StuttgartJamus a shekara ta 2009. A cikin shekara ta 2016, ta nuna ' yar kokawa ta Indiya, Geeta Phogat a fim din wasan kwaikwayo na Dangal wanda aka nuna a bikin Baje Kolin Kasa da Kasa na Beijing, kuma bikin BRICS na biyu.[4] Ta buga Zafira Baig, jarumi-maharbi Thug a cikin fim ɗin wasan kwaikwayo-haɗari, Thugs na Hindostan. Fatima sana Shaikh zata kasance a cikin shirin sake fim din Hindi na Aruvi na Tamil. Ana fitar da sigar Hindi ta Applause Entertainment.[5]
An haifi Fatima Sana Shaikh a cikin Birnin Hyderabad kuma ta tashi a Birnin Mumbai. Mahaifiyarta, Raj Tabassum, yar asalin Srinagar ce, mahaifinta kuma, wato Vipin Sharma, ya fito ne daga yankin Jammu.[6] A wata hira daga TheQuint.com, ta bayyana cewa yayin da mahaifinta ya kasance Hindu kuma mahaifiyarta musulma ce, Shaikh ta bayyana cewa bai yarda da addinin musulunci ba.[7]
↑"Fatima Sana Shaikh: Lesser known facts about the actress". The Times of India. TOI. Archivedfrom the original on 11 May 2019. Retrieved 17 April2019.
↑"Meet Aamir Khan's wrestler daughters". Mumbai Mirror. Archived from the original on 18 August 2016. Retrieved 31 March 2019.
↑Ghosh, Samrudhi (3 April 2019). "Fatima Sana Shaikh on her #MeToo story: It happened when I was very young". India Today. Delhi. Retrieved 19 August 2019.
↑Aneja, Atul (25 June 2017). "China's 'Dangal' mega-success echoes at second BRICS film festival". The Hindu. Archived from the original on 25 June 2017. Retrieved 19 August 2019.
↑Rathi, Vasundhara (20 December 2016). "Braving the bruises". The Hindu. Retrieved 26 September 2018.
↑"I am an atheist, I believe in karma: actress Fatima Sana Shaikh". The Siasat Daily. 29 October 2020. Retrieved 22 November 2020.
↑Rathi, Vasundhara (20 December 2016). "Braving the bruises". The Hindu. Retrieved 26 September2018.
↑"Screen Awards 2017 nominations announced". Screen. Retrieved 7 August 2021.
↑"Dangal girls Fatima Sana Shaikh and Sanya Malhotra win action award in China". Mid-Day. 23 July 2018. Archived from the original on 10 April 2019. Retrieved 9 April 2019.