Filin jirgin saman Maputo
Filin jirgin saman Maputo | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jiha | Jihar Enugu |
Babban birni | Enugu |
Coordinates | 6°26′39″N 7°29′47″E / 6.4442°N 7.4964°E |
History and use | |
Suna saboda | Nnamdi Azikiwe |
Wasa | ƙwallon ƙafa |
Occupant (en) | Enugu Rangers |
Maximum capacity (en) | 25,000 |
|
Filin wasa na Nnamdi Azikiwe filin wasa ne da ke da manufa da yawa a cikin jihar Enugu, Nigeria. A halin yanzu ana amfani dashi mafi yawanci don wasannin ƙwallon ƙafa kuma shine filin wasan gida na Enugu Rangers. Filin wasan yana daukar mutane guda 22,000 kuma an sanya masa sunan ne saboda shugaban kasa na farko na Jamhuriyar Najeriya, Dr. Benjamin Nnamdi Azikiwe.
Filin wasa na Nnamdi Azikiwe ya kasance mallakar kamfanin jirgin kasa na Najeriya (NRC). Har zuwa wannan lokacin shine mafi kyawun filin wasa a jihar Enugu.
Har zuwa shekara ta 1959, wurin shine filin wasanni na kamfani na Gundumar Gabas. Wannan ba abin mamaki bane kasancewar kamfani yana kan gaba wajen daukan wasabi gaba da bayan zamanin mulkin mallaka. Da lokaci ya ci gaba, a bayyane saboda matsayinta na musamman a tsakiyar Enugu, rusasshiyar Gwamnatin Gabashin Najeriya ta karɓi ragamar gudanar da wurin kuma ta ɗaukaka martabarta.
Sifiri
[gyara sashe | gyara masomin]Filin wasan ya ci gaba da aiki a matsayin wurin da ya tara ‘yan wasa da mata mazauna yankin na gabas, har zuwa barkewar yakin basasar Najeriya/Biafra. An sake sabunta shi bayan yakin basasa tare da dakunan kwanan dalibai don karbar 'yan wasa. Hakanan ya kunshi majalisar wasanni ta jihar.
Kungiyar Rangers International na Enugu suma an kafa su a lokacin kuma sun maida filin, filin-wasan gida. Rangers ta kara bunkasa cikin shekara ta 1970, musamman saboda kyawawan sakamako da suka sanya jim kaɗan bayan ƙirƙirar su.
Gini
[gyara sashe | gyara masomin]Daga baya anyi yunkurin sake Gina sabon filin wasan. Wannan ya haifar da kokarin hadin gwiwa daga tsohuwar Gwamnatin Jihar Anambra tare da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu don tara kudade don sake gina filin wasan, wanda aka kaddamar a cikin shekara ta 1986.
Shekaru goma sha uku bayan haka, an sake gyara filin wasan don samun daman ɗaukar nauyi gasan kwallon kafa ta duniya na kasa da shekaru 20, wato "FIFA U-20 World Cup" a Najeriya cikin shekara ta 1999. Ya buga muhimman wasanni ciki har da rashin nasarar da Najeriya ta yi a hannun Mali a wasan dab da na karshe.
Dausayi
[gyara sashe | gyara masomin]Filin wasan, wanda a baya yake da ciyawa na asali, a yanzu yana da shimfidadden ciyawan zamani wato "grass-kafet" da sabon allo na bidiyo. Waɗannan, da sauran ayyukan sabuntawa, an tsara su ne don ba filin wasan ƙarancin gine-ginen zamani da kere-kere saboda yana ɗaya daga cikin filin wasanni na FIFA U-17 World Cup Nigeria 2009.
Ta dauki bakuncin wasanni a rukunin D, wanda ya kunshi Turkiya, Costa Rica, Burkina Faso da New Zealand a gasar kwallon kafa ta duniya ta FIFA na 'yan wasa masu kasa da shekaru 17 wato "FIFA U-17 World Cup" a Najeriya a shekara ta 2009.