Godswill Akpabio

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Godswill Akpabio
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

13 ga Yuni, 2023 -
Ahmed Ibrahim Lawan
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

25 ga Faburairu, 2023 -
Christopher Stephen Ekpenyong
District: Akwa Ibom North-West Senatorial District
Minister of Niger Delta (en) Fassara

21 ga Augusta, 2019 - 11 Mayu 2022
Usani Uguru Usani - Umana Okon Umana (en) Fassara
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 - ga Yuni, 2019
District: Akwa Ibom North-West Senatorial District
Gwamnan Jihar Akwa ibom

29 Mayu 2007 - 29 Mayu 2015
Victor Attah - Udom Gabriel Emmanuel
District: Akwa Ibom North-West Senatorial District
Rayuwa
Haihuwa 19 Disamba 1962 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Mutanen Efik
Harshen uwa Ibibio
Ƴan uwa
Abokiyar zama Ekaette Unoma Akpabio
Karatu
Makaranta Jami'ar Calabar
Makarantar Koyan Lauya ta Najeriya
Government College Umuahia (en) Fassara
Harsuna Turanci
Ibibio
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
All Progressives Congress

Godswill obot AKpabio Con (an haife shi ranar 9 ga watan Disamba, 1962) dan siyasa ne na Najeriya kuma dan siyasa ne a halin yanzu shine Shugaban majalisar Dattijai ta 10 a Najeriya. Ya yi aiki a matsayin Sanata mai wakiltar Akwa Ibom Arewa maso Yamma daga shekara ta, 2015 zuwa 2019 da kuma 2023. Ya kuma rike mukamin minista a harkokin Neja Delta daga Shekara ta, 2019 zuwa 2022. Yayi gwamnan jihar Akwa Ibom daga shekara ta, 2007 zuwa 2015.[1]

Karatu da Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Akpabio ya yi karatu a Makarantar Firamare ta Methodist, Ukana,  Essien Udim LGA,  Jihar Akwa Ibom; a Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Port Harcourt, Jihar Rivers; da Jami'ar Calabar, Jahar Cross River, inda yayi digiri a fannin shari'a. Gyaran sana'a da aiki

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Matsayin malami kuma a matsayin abokin hulda da jama'a tare da Paul Usoro & Co., wani kamfanin doka a Najeriya.

Mukamin Gwamnati[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar, 2002, Gwamna Obong Victor Attah ya nada shi Honourable Commissioner na Man Fetur da Albarkatun kasa a jihar Akwa Ibom. Tsakanin shekara ta, 2002 zuwa 2006, ya yi aiki a matsayin kwamishina a ma'aikatu uku masu mahimmanci: Man Fetur da Albarkatun ƙasa, Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, da Filaye da Gidaje.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta, 2006, ya yi sha’awar tsayawa takarar gwamna a jihar Akwa Ibom a zaben fidda gwanin da aka fafata tare da doke wasu ‘yan takara 57 da suka yi takara a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).Yaƙin neman zaɓen da ya yi mai taken, “a yi nufin Allah” ya sami goyon bayan jama’a kuma aka zabe shi Gwamna a shekarar, 2007. An sake zaɓe shi a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Akwa Ibom a shekarar, 2011.

a shekarar, 2013, an zabe shi a matsayin Shugaban sabuwar kungiyar Gwamnonin PDP.

Takarar Sanata[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar, 2015, ya tsaya takarar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma (Ikot Ekpene) don wakiltar gundumar a Majalisar Dattawan Tarayyar Najeriya. Da yake takara a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), ya samu kuri’u 422,009 daga cikin 439,449 inda ya doke Cif Inibehe Okorie na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 15,152 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana. An zabi Akpabio a matsayin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa wanda ya fito daga Kudu-maso-Kudu a Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda jam’iyyar PDP ta amince da shi a Majalisar Dattawa kuma Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana shi a matsayin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa ranar 28 ga Yuli shekara ta,2015. PDP ta rasa rinjaye a hannun jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben shekara ta,2015.

A watan Agustan shekara ta,2018, ya yi murabus a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattijai, bayan ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress. Ya sauya sheka ya yi gangamin siyasa a mahaifarsa a filin wasa na garin Ikot Ekpene, jihar Akwa Ibom. A watan Yulin shekara ta, 2019 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabe shi kuma majalisar dattawan Najeriya ta tantance shi domin a nada shi minista. A ranar 21 ga Agusta shekara ta, 2019, an rantsar da shi a matsayin ministan harkokin Neja Delta.

A watan Yunin shekara ta,2022, Akpabio ya yi murabus daga mukaminsa na ministan harkokin Neja Delta domin ya tsaya takara a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki amma ya sauka a daren da aka gudanar da zaben fidda gwani wanda Bola Tinubu ya lashe. Kwanaki kadan bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa, ya fito a matsayin dan takarar Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma. Sai dai kuma yana cike da zarge-zargen da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar ke yi. Ya kayar da abokin hamayyarsa Emmanuel Enoidem na jam’iyyar Peoples Democratic Party ya zama zababben Sanata a zaben shekara ta,2023 inda ya samu kuri’u 115,401, inda Enoidem ya samu kuri’u 69,838.[2]

A ranar 13 ga watan Yunin shekara ta, 2023 ne aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya da kuri'u 63 inda ya doke Sanata Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara wanda ya samu kuri'u 46.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]