Jump to content

Grace Ekpiwhre

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Grace Ekpiwhre
mutum
Bayanai
Jinsi mace
Ƙasar asali Najeriya
Suna Grace
Shekarun haihuwa 4 ga Janairu, 1949
Wurin haihuwa Ethiope ta Yamma
Harsuna Turanci da Pidgin na Najeriya
Sana'a ɗan siyasa da civil servant (en) Fassara
Muƙamin da ya riƙe Minister of Science and Technology (en) Fassara da Minister of Works and Housing (en) Fassara
Ilimi a Jami'ar jahar Lagos

Grace Ekpiwre (ranar 4, ga watan Janairun 1949), ma'aikaciyar gwamnati ce wacce ta yi ritaya a cikin shekarar 2007. Shugaba Umaru Ƴar'aduwa ne ya naɗa ta a matsayin ministar kimiyya da fasaha ta Najeriya a cikin watan Yulin 2007, sannan ta zama ƙaramar ministar ayyuka, gidaje da raya birane a cikin watan Disamban 2008.[1]

Rayuwar farko da ilimi.

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Grace Ekpiwhre a ranar 4, ga watan Janairun 1949, a ƙauyen Ikweghwu a Agharho, cikin ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta. Ta girma a wani ƙauye mai suna Ovu Inland a Ethiope West, Jihar Delta. Ta halarci Makarantar Apostole ta Our Lady of Apostle, Ijebu-Ode, Jihar Ogun tsakanin shekarar 1962, zuwa 1966, da Kwalejin Gwamnatin Tarayya Warri daga 1967, zuwa 1968. Ta halarci Jami'ar Legas, inda ta kammala karatun BSc Zoology a cikin watan Yunin 1972.[2]

Aikinta na farko shine da ma'aikatan gwamnati na jihar Bendel a matsayin jami'in Kifi na Grade II. Ta ci gaba da matsayi, inda ta riƙe muƙamai da suka haɗa da Darakta Janar na Harkokin Mata da Darakta Janar na Gwamnatin Parastatals. Ta zama Sakatare na dindindin a cikin shekarar 1999, a wani lokaci mai kula da Gidaje. An naɗa ta shugabar ma’aikatan gwamnati, jihar Delta a cikin shekarar 2002, da kuma shugabar hukumar ma’aikata a cikin shekarar 2007.[1][3]

Naɗin siyasa.

[gyara sashe | gyara masomin]

An naɗa Grace Ekpiwhre Ministar Kimiyya da Fasaha a cikin watan Yulin 2007.[4] Bayan da aka yi wa majalisar ministoci garambawul a cikin watan Disambar 2008, an naɗa ta ministar ayyuka, gidaje da raya birane.[5]