Jump to content

Hajara Ibrahim Ɗan'azumi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hajara Ibrahim Ɗan'azumi
Rayuwa
Haihuwa 2005 (18/19 shekaru)
Sana'a

Hajara Ibrahim Ɗan'azumi mahaddaciyar Alqur'ani mai girma wadda ta fito daga jihar Gombe, Najeriya. itace wacce ta lashe gasar Kur'ani ta 2024 da aka gudanar a Masarautar Jordan, A cikin 18th edition na Hashemite Jordan gasar ƙasa-da-ƙasa ta Alqur'ani Qur'anic ta mata, inda ta doke abokan fafatawarta 41 daga ƙasashe 39. Ta shiga cikin gasar Alqur'ani da da yawa a duk fadin kasar. A shekarar 2015, ta sami matsayi na 2 a gasar Kur'ani ta kasa da aka gudanar a Jihar Edo. Bugu da ƙari, ta sami matsayi na 3 a gasar Alkur'ani ta kasa da aka gudanar a Katsina. Wasu gasa, ta sami matsayi na 4 da 5 a Legas da Kano, bi da bi.[1][2][3]

Rayuwar farko da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Hajara a jihar Gombe cikin babban birnin Gombe a unguwar tudun Wada bayan gandu. Kuma ta halarci makarantar Darul Arqam Academy, inda ta yi karatun firamare da Haddar Alqur'ani da kuma ilimin addinin Muslunci duka. Bugu da ƙari, ta halarci Bin Malik Islamiyya, Makarantar Musulunci ta Abubakar Siddiq duk suna cikin jihar Gombe. A halin yanzu, ita daliba ce mai karatun digiri a matakin aji na 200 watau a turance ake kira da 200 level a Jami'ar Jihar Gombe.

Kyaututtuka[gyara sashe | gyara masomin]

Hajara, wadda ta lashe gasar alkur'ani ta duniya da aka gudanar a Jordan daga watan Fabrairu 17 zuwa 22, 2024, Hukumar Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ba ta kujerar Hajji kyauta.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Gimba Yaya, Haruna (27 February 2024). "Nigerian Girl Wins Qur'an Recitation Competition In Jordan". dailytrust.con. Retrieved 10 March 2024.
  2. "Gwamnan Gombe ya jinjina wa yarinyar da ta lashe gasar karatun Al-Ƙur'ani ta duniya". BBC Hausa. 27 February 2024. Retrieved 10 March 2024.
  3. "Jordan Int'l Quran Contest for Women Awards Winners". Iqna. 24 February 2024. Retrieved 14 March 2024.