Jump to content

Hamid Algabid

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hamid Algabid
firaministan Jamhuriyar Nijar

14 Nuwamba, 1983 - 15 ga Yuli, 1988
Mamane Oumarou - Mamane Oumarou
Member of the National Assembly of Niger (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Belbédji (en) Fassara, 1941 (82/83 shekaru)
ƙasa Nijar
Karatu
Makaranta Jami'ar Félix Houphouët-Boigny
Thesis director Christian Gavalda (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Kyaututtuka
Imani
Jam'iyar siyasa Rally for Democracy and Progress (en) Fassara

Hamid Algabid (anhaifeshi 1941) dan siyasar kasar Nijer ne kuma shugaban jam'iyyar (RDP Jama'a da Hausanci, Rassemblement pour la démocratie et le progrès da Faransanci). Lauya, Ma'aikacin banki Algabid ya kasance muhimmi a tafiyar tsohon firaminista Seyni Kountché, tsakanin 1983-1988. Ya rike matsayin babban mai magana da yawun kungiyar Musulmai ta duniya wato Organisation of the Islamic Conference (OIC) tsakanin 1989 zuwa 1996, kuma tun daga 1996 shine shugaban jam'iyar RDP (jama'a).

Farkon rayuwar sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Dan kabilar Abzinawa ne, anhaifi Algabid a karamin kauyen Belbeji, kusa da garin Tanout shekarar 1941.[1] Ya karanci ilimin shari'a a Jami'ar Abidjan ta kasar Kwaddibuwa da kuma a kasar Faransa. Ya ruke mukaman shugaban bangare da babban sakatare a ma'aikatar tattara kudin shiga ta kasar Nijar.[2]

  1. Cherif Ouazani, "Six candidats pour un fauteuil" Archived 2007-09-30 at the Wayback Machine, Jeune Afrique, 7 November 2004 (in French).
  2. Decalo, Samuel (1997). Historical Dictionary of the Niger (3rd ed.). Boston & Folkestone: Scarecrow Press. ISBN 0-8108-3136-8.:pp.32–33