Harin bam a Abuja, Oktoba 2010

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentHarin bam a Abuja, Oktoba 2010
Iri aukuwa
Kwanan watan 1 Oktoba 2010
Wuri Abuja
Adadin waɗanda suka rasu 12
Adadin waɗanda suka samu raunuka 17

Tashin bama-bamai na watan Oktoba a shekara ta 2010 a Abuja, Wanda ake kuma kira da tashin bama-bamai a ranar ƴancin kai na Najeriya a shekarar 2010 , wasu hare-haren bam ne da mota guda biyu da aka kai kan jama’ar da ke bikin cika shekaru hamsin da samun ‘yancin kai a babban birnin tarayya Abuja da safiyar ranar 1 ga watan Oktoba, 2010. Hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 12 tare da jikkata 17. A cewar majiyoyi da yawa,[1][2] ƙungiyar Movement for the Emancipation of the Niger Delta (MEND) ta yi gargadi ƙasa da sa'a guda kafin tashin bom na farko da ya fashe, kusa da dandalin Eagle Square (wuri na bikin), sai kuma, wajen ƙarfe 10:30 na safe, sauran bama-bamai suka tashi.[3]

Fashewar farko ta faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe, jami'an agajin gaggawa sun isa wurin sannan kuma fashewa ta biyu ta afku biyo bayan fashewar bom na farko.[2]

Amsa da bincike[gyara sashe | gyara masomin]

An kama wani tsohon shugaban ƙungiyar MEND, Henry Okah a ƙasar Afirka ta Kudu bayan tashin wasu tagwayen bama-bamai a cikin mota.[4] Okah ya musanta zargin da ake masa na shirya tashin bama-bamai kuma ƙungiyar MEND ta musanta.[5] Ƴan sanda a Najeriya sun kuma tsare Raymond Dokpesi, manajan yaƙin neman zaɓen tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Babangida, domin amsa tambayoyi kan tashin bam ɗin. Daga baya an saki Dokpesi ya ce kama shi batu ne na siyasa.[6]

Jaridar This Day ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, an gargaɗi jami'an leken asirin Birtaniyya game da shirin shirya bikin cika shekaru 50-(da samun ƴancin ƙasar), kuma wannan ne dalilin da ya sa tsohon Firayim Minista Gordon Brown da Yarima Richard, Duke na Gloucester suka soke tafiye-tafiyen da suka shirya zuwa Najeriya domin bikin.[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Nigeria: Death toll in bombings rises to 12". Associated Press. 2010-10-02. Retrieved 2010-10-02.
  2. 2.0 2.1 BBC News (2010-10-02). "UK VIPs pulled out ahead of deadly Nigeria parade". BBC News. Retrieved 2010-10-02.
  3. Weate, Jeremy (2010-10-01). "Nigeria explosion: Independence celebrations marred by violence". The Christian Science Monitor. Retrieved 2010-10-02.
  4. "Nigeria ex-rebel leader Okah arrested after Abuja blast". Archived from the original on 2010-10-06. Retrieved 2010-10-11.
  5. Suspect in Nigeria Blast Disowned by Niger Delta Militants
  6. Nigeria: My Ordeal With SSS Over Abuja Bombings, By Dokpesi
  7. Nigeria: British Intelligence Warned of Attacks