Harin bama-bamai a Najeriya, Mayu 2011
Iri |
bomb attack (en) aukuwa |
---|---|
Kwanan watan | 29 Mayu 2011 |
Wuri |
Abuja Zariya Bauchi Maiduguri |
Adadin waɗanda suka rasu | 15 |
Adadin waɗanda suka samu raunuka | 55 |
Perpetrator (en) | Boko Haram |
Hare-haren bam da aka kai a arewacin Najeriya a watan Mayun 2011 ya abku a wasu garuruwan da ke arewacin Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun 2011. Fashe-fashen sun faru ne sa'o'i kaɗan biyo bayan rantsar da Goodluck Jonathan a matsayin shugaban Najeriya. [1] Ana zargin ƙungiyar Boko Haram da alhakin kai hare-haren. [2]
Fashewar farko ta afku a kasuwar Zuba da ke Abuja, inda mutane biyu (ciki har da wata yarinya) suka mutu tare da jikkata wasu su 11. Har ila yau wasu bama-bamai uku sun tashi a kasuwar Mammy da ke Bauchi, kusa da hedkwatar runduna ta 33 ta artillery ta Najeriya. Mutane 13 ne suka mutu sannan wasu su 40, suka jikkata. [1] Babu wani soja da ya jikkata. [3] Har ila yau bama-bamai biyu sun tashi a Zariya, inda mutum huɗu suka samu munanan raunuka. [1]
Wani fashewar wani abu ya rutsa da motar sojoji a Maiduguri. [1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 Bomb blasts rock Nigeria, 15 killed, 55 injured Daily Independent, 30 May 2011.
- ↑ More bombs follow Nigeria inauguration UPI, 30 May 2011.
- ↑ 13 Killed, 40 Injured in Bauchi Bomb Tragedy